Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Ban taba jin wata kyakyawar gwamanti a Najeriya ba – Young

Mista Andrew Young

Ban taba jin wata kyakyawar gwamanti a Najeriya ba – Young

Tsohon Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Mista Andrew Young ya ce baya jin dadin yadda al’ummar Najeriya ke sukar gwamnatocin kasar, domin babu wani tsarin gwamnati a duk duniya da yake cikakke,

Jakada Young ya ce “Akwai bukatar ’yan Najeriya su yi aiki tukuru da sadaukar da kai domin ganin sun ci sakamakon aikin da suka yi, kuma su kauce wa ’yan a fasa kowa ya rasa, Young yana bayani ne a birnin Abuja a wata liyafa da aka shirya domin bikin cika shekara uku na nasarar da Gidauniyar Emeka Offor ta samu, kan rashin bullar cutar shan inna a Najeriya.

Bikin ya samu halartar manyan baki da suka hada da Ministan Watsa Labarai, Alhaji Lai Mohammed.  A ranar Larabar makon jiya ne Najeriya ta cika shekara uku ba a samu rahoton bullar cutar shan inna ba.

Jakada Young ya kara da cewa “Ku ’yan Najeriya a kullum kuna korafi a kan kowace gwamnatinku, wanda tunda nake ban taba jin cewa ga wata ingantatciyar gwamnati gare ku ba, ku tuna kowa yana da nasa aibun, dole ne mu fuskanci gaskiya, duniyar nan babu wanda zai ce shi goma yake, amma dai akwai mutane da ke da yakinin yin aikin haikan da kuma sadaukar da kai domin ci gaban kasa, akwai al’ummar da ke shan wahalar rayuwa fiye da ku mutanen Najeriya.”

Ya ce ’yan Najeriya ba wawaye ba ne, “Hazikan mutane da na taba ganin a rayuwata, kuma a kullum suna cikin burin su sadaukar da kansu domin ci gaban kasarsu, hakan ya sa nake martaba Sa Emeka Offor domin ya yi hakan kowa ya gani.

A wani labarin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ilimi da kiwon lafiya su ne abubuwan da gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa fifiko. Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata lokacin da Mista Andrew Young ya ziyarce shi a fadarsa a birnin Abuja.