✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bana za mu yi dalar masara a Saminaka – Tasi’u Bako

Alhaji Tasi’u Bako Na-Bawa shi ne  Shugaban Kungiyar Noma Don Riba a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna. Yana daya daga cikin matasan da suka…

Alhaji Tasi’u Bako Na-Bawa shi ne  Shugaban Kungiyar Noma Don Riba a garin Saminaka da ke Jihar Kaduna. Yana daya daga cikin matasan da suka yi fice, a harkar noma a yankin Saminaka. A tattaunawar da ya yi da wakilinmu, ya ce bana za su yi dalar masara a yankin da ya yi suna a noman masaraa kasar nan:

Me kake ganin ya karfafa wa al’ummar yankin Saminaka rungumar harkokin noma?

Tasi’u Bako: Wato  mutanen wannan yanki suna da rabo kan noma. Kuma ka san shi noma rubutu ne daga Allah, duk kwarewarka da iyawarka idan Allah bai sa kana da rabo a kai ba, ko ka yi gonar sai kag a Allah Ya sako maka wani iftila’i ya shigo. Don haka wannan noma da ake yi a wannan yanki, wani abu ne daga Allah.

A duk Najeriya babu garin da za ka je ka tarar da dan shekara 30 zuwa 34 yana noma masara fiye da buhu dubu 10, kuma ya noma  wake sama da buhu dubu daya babu saka hannun kamfani ko tallafin banki ko gwamnati, sai a wannan yanki na Saminaka.

Saboda haka, duk mutumin da ka gani a wannan yanki ya dogara ga Allah ne, kuma ya dogara ga noma. Don haka a wannan yanki babu abin da za mu ce wa Allah, sai dai mu kara yi masa godiya. Domin Ya yi mana albarkar kasa da ruwa da muke wannan noma.

Me ya sa manoman yankin suka fi rungumar noman masara?

Tasi’u Bako: Babban dalilin da ya sa manoman wannan yanki suka fi mayar da hankali kan noman masara, shi ne nazarin da aka yi tunda da ya nuna cewa idan aka shuka masara a yankin tana yin kyau. Domin wannan yanki yana daya daga wuraren da suka dace da noman masara a duniya ba a Arewa, ko Najeriya  kadai ba. Saboda haka wannan ya kara wa manoman yankin karfin gwiwa, wajen rungumar noman masara.

Akwai mutane da dama da suka yi fice kan noman masara wadanda suke raye da kuma  wadanda suka rasu.  Cikin manoman masara da suka yi fice a wannan yanki da suka rasu akwai irin su Alhaji Rayyanu Dan Alhaji da Alhaji Abdu Kwaki da Mato Anana da sauransu. Cikin manoman masarar da suke raye  akwai irin su Alhaji Sa’idu Sarkin Noma Sigau da dansa Alhaji Kamilu Sa’idu da Alhaji Ibrahim Dokar Dan Bala da Alhaji Abdul’aziz Gidan Dutse da sauransu. Babu shakka wannan yanki ya shahara kan noman masara. Don haka a bana muna shirye-shiryen yin dalar masara a wannan yanki, wadda ba a taba yi ba a Najeriya. Muna sa ran za mu gayyato Ministan Gona domin  ya zo ya kaddamar da dalar masarar,da za mu yi. Masarar da ake nomawa a yankin nan ana kai ta kasashen Chadi da Kamaru da ko’ina a Najeriya.

Saboda noman masara da muke yi,  duk kamfanonin taki a Najeriya suna tutiya da yankin  wajen ciniki. Domin akalla mu ne muke sayen kashi 80 cikin 100 na takin da ake sayarwa a Najeriya.

Ba noman masara kadai ba, a da ana tinkahon cewa mutanen Makarfi ne suka yi fice, kan noman rake a Jihar Kaduna. A yanzu mutanen yankin nan sun kwace wannan matsayi, domin yanzu a yankin Saminaka akwai mutum daya da na sani a gonarsa ta rake, ana cire sama da tilera 400. Yanzu a kullum a yankin akalla ana loda motar rake 50, zuwa sassan Najeriya da kasashen waje.

Don haka duk wani irin gida a Najeriya, manoman suna ginawa a yankin Saminaka. Manomin wannan yanki zai sayo sabuwar mota ful a leda, kamar yadda ma’aikatan gwamnati da ’yan siyasa da  kamfanoni suke yi. Idan ka kalli yadda ake biyan kudin kujerun aikin Hajji, manoma ne kan gaba a wannan yanki.

Wace gudunmawa manoman yankin suke bayarwa ga bunkasa tattalin arzikin kasar nan?

Tasi’u Bako: Idan muka dubi maganar inganta tattalin arziki tsakani da Allah mutanen yankin Saminaka, suna bada gagarumar gudunmawa. Domin akwai kamfanoni da dama a Najeriya da suka dogara da yankin wajen samun kayayyakin da suke sarrafawa. Kamar abin da ya shafi masara da waken soya da dawa da sauran kayayyakin amfanin gona.

Wadanne matsaloli suke damun manoman yankin?

Tasi’u Bako: Babbar matsalar manoman wannan yanki ita ce rashin masu zuba jari daga waje. A kullum muna janyo hankalin gwamnati kan ta kawo mana masu sanya jari kan harkokin noma daga kasashen waje, domin su zo su kafa mana masana’antun sarrafa kayayyakin amfanin gona a yankin. Yin haka zai dada karfafa wa manoman yankin gwiwa su ci gaba da noma.

Wace gudunmawa kake ganin harkokin  noma ke  bayarwa wajen samar da ayyukan yi ga matasa?

 Tasi’u Bako: Idan gwamnati ta inganta noma a kasar nan, za a bai wa kowane dan Najeriya aiki. Domin a duk duniya babu abin da yake bayar da ayyukan yi kamar noma.