✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bankin duniya zai ba da bashin dala miliyan 400 don inganta noman rani

Bankin duniya zai bayar da rancen kudi kimanin Dala miliyan 400 don farfado da noman rani da sun kifi a kogunan Hadejiya da Sakkwato da…

Bankin duniya zai bayar da rancen kudi kimanin Dala miliyan 400 don farfado da noman rani da sun kifi a kogunan Hadejiya da Sakkwato da Rima da na Bakalori da kuma wuraren noman rani na jihar Kano.
Jagoran tawagar Bankin Duniya da suka kai ziyarar gani da ido wuraren noman rani da na Hadejiya Mista Dabid Casanoba ne ya bayyyana hakan, inda ya yi nuni da cewa “makasudin ziyararmu shi ne don mu gane wa idonmu irin matsalolin da ayyukan noman ranin ke fuskanta, sannan mu tattauna da masu amfani da ruwan kogin wajen noma da kamun kifi, kafin mu kammala yarjejeniyar ba da rancen.”
Ya kara da cewa, tawagar tasu ta gamsu da abubuwan da suka gani, sannan kuma za su rubuta rahotonsu don mikawa gaba. Kuma suna sauraron samun wani rahoton daga hukumar albarkatun ruwa ta kasa don kammala yarjejeniyar samar da rancen.
Shi kuwa jagoran tawagar hukumar albarkatun ruwa ta kasa, Injiniya R.A. Oyewole bayyana gamsuwarsa ya yi da ziyarar ta jami’an bankin na duniya, ya ce zuwan nasu zai ba su damar ganin
zahirin matsalolin da ke fuskantar hanyoyin ruwa da kogunan wadannan yankuna da suka hada da ciyawar Kacalla da ke hana ruwa gudu yadda ya kamata.
Shi kuma manajan gudanarwa na hukumar kogunan Hadejiya-Jama’are, Alhaji Abdu dahiru, ya bayyana cewa madatsar ruwa ta kogin Hadejiya tana iya samar da lita miliyan 24 na ruwa, amma a saboda matsalolin da take fuskanta, yanzu tana iya samar da lita miliyan 8 ne kawai. Ya kuma ce
kimanin mazauna gabar ruwan su miliyan 20 ne suke amfana da ruwan madatsar, wajen noman rani da kamun kifi.