✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barccelona na zawarcin dan kwallon Najeriya Chukwueze

Rahotannin da ke fotwa daga kulob din FC Barcelona na Spain sun ce akwai yiwuwar kulob din ya kulla yarjejeniya da dan kwallon Super Eagles …

Rahotannin da ke fotwa daga kulob din FC Barcelona na Spain sun ce akwai yiwuwar kulob din ya kulla yarjejeniya da dan kwallon Super Eagles  ta Najeriya, Samuel Chukwueze da yanzu haka ke buga kwallo a kulob din Billareal na Spain.

Dokar La-Liga ta Spain ta amince kowane kulob zai iya sayo dan kwallo daya a gasar La-Liga ta Spain muddin dan kwallonsu ya ji raunin da zai sa ya shafe akalla wata shida a benci.

Barcelona dai ta rasa dan kwallon gabanta  Osumane Dembele ne bayan ya ji raunin da zai sa ya yi jinyar wata shida.

Ganin kulob din ya shiga cikin wannan matsala ce ya sa ya nemi izini daga hukumar kula da gasar La-Liga don a sahale masa ya sayo dan kwallon da zai maye gurbin Dembele duk da an rufe kasuwar cinikin ’yan kwallo a watan jiya.

Rahotanni sun ce Samuel Chukwueze da yanzu ke da kwantaragi da Billareal akwai yiwuwar kulob din ya sayar da shi ga FC Barcelona idan aka yi musu gwaggwaban tayi.

Chukwueze dai yana daga cikin ’yan kwallon Najeriya Super Eagles