Da Dumi Dumi

Barka Da Sallah Gizagawan Najeriya

Wasu daga cikin Gizagawan Zumunci tare da Babban Jojin Jihar Katsina, Mai Shari’a Xanladi Abubakar, bayan kammala taro a Katsina kwanakin baya

Ya ku Gizagawan Zumunci, barkanmu da wannan lokaci, barkanmu da ganin karshen watan Azumi lafiya. Muna rokon Allah Ya amshi ibadojinmu, Ya sake nufa mu ga wasu watannin Azumin na badin badada. ’Yan uwana Gizagawa da dukkan al’umma, Barka Da Sallah!

A yayin da muke bukukuwa da rugundumin Sallah, kada mu mance darussan da muka kowa cikin Azumi. Mu siffatu da dibiya dukkan darussan cikin mu’amalolinmu da ayyukanmu na rayuwar yau da kullum.

A lokacin Azumi, mun koyi hakuri da juriya, don haka sai mu ci gaba da nuna wadannan muhimman halaye a kowace mu’amalarmu. Idan aiki muke yi ko sana’a, mu kasance masu hakuri da abokan aikinmu ko sana’armu. Mu kasance masu juriya da mayar da hankali ga dukkan abin da muke yi. Ta haka ne za mu samu nasarar rayuwa.

A lokacin Azumin da ya gabata, mun koyi kyautata mu’amala, mun nuna kauna da son juna da zumunci. A wannan karon ma, sai mu ci gaba da haka. Kada mu yanke zumunci, mu ci gaba da jaddada shi. Mu riki juna da kauna da soyayya.

Miji da mata, saurayi da budurwa, aboki da aboki, kawa da kawa, makwabci da makwabci, mu zauna lafiya, mu dauki darussan Azumi na jaddada salama da aminci tsakanin juna. Mu kauce wa husuma da tashin hankali da juna. Mu tanadi halaye da matakan kyautata wa juna da tattalin juna, yadda za mu kasance cikin amincin juna da zaman lafiya.

ADVERTISEMENT

A yayin da al’ummarmu, musamman na yankin Arewa maso gabas ke fuskantar matsalolin ta’addancin Boko Haram da garkuwa da mutane da kashe-kashe da kone-konen rayuka da dukiya, mu tausaya musu, mu jajanta musu, mu ci gaba da bibiyarsu da addu’a. Allah Ya kawo mana sauki, Ya ba gwamnatinmu ikon dakile wannan mummunan al’amari, amin. Barka Da Sallah!

***

Shugabannin Gizagawa na Jihohi daban-daban sun aiko da sakonnin Barka Da Sallah ga daukacin Gizagawan Najeriya da sauran al’umma gaba daya, don haka ga abin da suke cewa:

Daga Hedikwatar Jihar Filato, wato Jos, Shugaban Gizagawan jihar, Kabeer SKB Rikkos Jos (08068362204), ya bayyana sakon Barka Da Sallah, inda yake cewa: “A madadin Gizagawan Jihar Filato, muna yi wa Gizagawan Najeriya Barka Da Sallah; da fatan za a yi shagalin Sallah lafiya. Ina manyan Gizagawa, to ku farka domin zumunci ya dawo!”

Daga Jihar Legas kuwa, Bagizage Malam Rabi’u Yunus Agege ya bayyana cewa: “Assalamu alaikum. A madadina da Gizawan jiharmu ta Legas, muna yi wa shugabanninmu na kasa da kuma al’ummar Musulmin duniya Barka Da Sallah. Allah Ya maimaita mana, amin.”

Daga Jihar Kano, sakon Gizagawa ya zo daga Malam Kabiru Ghali AbbanSaudat; wanda ya ce: “Assalamu alaikum. Sunana Kabiru Ghali Abban Saudat. Ina mika sakon gaisuwar Barka Da Sallah ga iyayena da ’yan uwana, sannan ina isar da sakon gaisuwar Barka Da Sallah ga Malam Nura Adamu Ahmad da Hajiya A’isha Lawal Tarauni da Halliru Kabir Gogel da Abdul’ziz Bakamaula da Abdu Goro, da sauran ’yan uwa Gizagawa na Jihar Kano da kasa baki daya; da fatan mun yi Sallah lafiya!”

Sai kuma sako daga Gizagawan Jihar Kaduna, ta bakin Bagizage Malam Zakariyya Sa’eed Abu-Hafsat, wanda ke cewa: “Assalamu alaikum, Maigida barka da maraice da fatan kai da dukkan iyalanka kuna nan lafiya. Sakon Barka Da Sallah gare ka da dukkan Gizagawan Zumunci. Ina fatan an yi Sallah lafiya, Allah Ya maimaita mana ta badin badada.”

Sai kuma Comrade Yusuf Lawal Amaru Zariya (07038994676), wanda ke cewa: “A madadin ni kaina da iyalaina, muna mika sakon taya murna ga daukacin Gizagawan Najeriya, tare da daukacin jama’ar Musulmi, na kammala Azumin watan Ramadan lafiya. Muna fatan Allah Ya sa mun dace da alherin da ke cikin watan na Ramadan. Muna fatan za a yi Sallah cikin koshin lafiya, Allah Ya taimake mu, amin. Na gode.”

Haka shi ma Adamu Usman Katsina (08169957978), ya bayyana farin cikinsa kamar haka: “Assalamu alaikum. A madadi na da iyalina, ina taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar Idin Sallah karama, da fatan Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta mana laifukanmu, amin.”

***

Hakika Gizagawa kun kyutata zumunci, Allah Ya biya. Barka Da Sallah! – Gizago.

 

Share