✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bata-gari sun mayar da kasuwa wajen cinikin miyagun kwayoyi

Ana zargin wasu ‘yan kasuwan sSabon garin Zariya da neman maida  kasuwar ta zama sansanin sayar da miyagun kwayoyi. Matsalar ta’annadi da miyagun kwayoyi da…

Ana zargin wasu ‘yan kasuwan sSabon garin Zariya da neman maida  kasuwar ta zama sansanin sayar da miyagun kwayoyi.

Matsalar ta’annadi da miyagun kwayoyi da kayan maye a tsakanin matasa  da matan aure na kara yawaita a yankin Zariya da kewaye.

Hakan na faruwa ne a bisa zargin da ake yi  na  yadda kusan mafiya yawan masu gudanar da sayar da haramtattun magunguna da kwayoyi da Gwamnatin Jihar Kano ta koro ne suka dawo da matsuguninsu a kasuwar sabon garin Zariyan, wanda hakan ya sanya damuwa a zukatan al’ummar yankin.

Majiyarmu da ta tabbatar wa Aminiya, kuma wadanda ba su so a ambaci sunayensu ba, kuma suna daga cikin ‘yan kasuwan wasunsu ma ‘yan kwamitin zartarwa ne  na masu sayar da magunguna a kasuwar, wanda wakilin namu ya tattauna da su cewa akwai korafe-korafe da dama akan haka, sai dai suna so jama’a su sani cewa  korarrun masu sana’ar  sayar  da  magunguna na Kano da gwamnatin jihar ta kora sune suka dawo kasuwar Sabon garin na Zariya, kamar Mista Jude da  Lambat da kuma Donotus  da Bitrus,  kuma  wadanda ake zargin  suna da hanyoyin da suke bi don shigowa da wadannan haramtattun miyagun magunguna ba tare da an kama su ba, domin sukan sanya kwayoyin a kwalayen da ba za’a taba zaton suna ciki ba, kuma wani lokaci ba sa zuwa kasuwar sauke kayan sai da daddare,  kuma da damar mu musan da haka sai dai mun yi kokarin  jawo,  ko  shawartar shugabanmu, amma ya ki fahimta. 

Don haka ka ga jama’a  suka hadamu gaba daya suna yi mana kakkabar dan  giginya an hada mu gaba daya cewar duk haka muke.

Kamar yadda a duk lokacin da Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris in yana jawabi yake kokawa da yawan ta’annati da miyagun kwayoyi  da kayan sanya maye a tsakanin matasa da matan aure, tare da yin kira ga hukumomin da su  kara kaimi, domin dakile ire-iren masu tafiyar da wannan mummunar sana’ar don ceto al’umma daga halaka.

Da Aminiya ta tuntubi Shugaban  masu sayar da magani na kasuwar Sabon gari Zariya, Alhaji Rabiu Kaya ta wayar hannu ko yana da masaniyar irin abin da ke faruwa a kungiyarsu, sai ya amsa da cewa shi a saninsa da ana shigowa da irin wadannan miyagun kwayoyin, amma yanzu ba a shigowa da su, kuma idan muna wata tantama to mu zo mu yi bincike, domin  ya gaji da bita-da-kullin da ‘yan jarida ke yi musu saboda haka ba shi da abin da zai kara cewa sai dai suna shirin daukar duk wani mataki  da ya dace a kan ‘yan jarida ta kowane  irin hanya, domin sun matsa musu tare da sa musu idanu akan sana’arsu.