✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun bashin Naira biliyan uku na kananan hukumomin Bauchi ya tayar da kura

Bayanan da Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Bauchi ta yi cewa  tana kokarin kawar da bashin Naira biliyan uku da ta yi zargin cewa tsohuwar…

Bayanan da Ma’aikatar Kananan Hukumomi ta Jihar Bauchi ta yi cewa  tana kokarin kawar da bashin Naira biliyan uku da ta yi zargin cewa tsohuwar gwamnatin jihar ta sanya asusun kananan hukumomi 20 a hannun banki, lamarin da ta ce na kawo tarnaki wajen tafiyar da harkokin kananan hukumomin sun tayar da kura, inda daya daga ciikin tsofaffin shugabannin riko na kananan hukumomin ya ce an sanya siyasa a maganar.

Kwamishinan Ma’aikatar Alhaji Abdulrazak Nuhu Zaki ne ya tado batun lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, inda ya ce gwamnatin da ta wuce ta sanya asusun kananan hukumomi kan wani layi na rance ta yadda a kullum kudaden kananan hukumomi suke shiga asusu, sai kawai bankin ya kwashe  ya bar su ba su da wani abu da za su iya gudanarwa.

Kwamishina Zaki ya ce  bashin ya dame su kwarai don ana biyan kudin ruwa kimanin kashi 18 da bankin ke dauka kan rancen. Ya  kuma ce duk da dimbin kudin da Gwamnatin Tarayya ke bayarwa, sai da aka ciwo bashin da yake damunsu yanzu.

Ya ce tun lokacin da ake yakin zabe, Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya yi alkawarin cewa zai gudanar da zaben kananan hukumomi cikin shekara guda, bayan dawo musu da martabarsu da darajarsu da ya yi zargin tsohuwar gwamnatin ta lalata. “Amma kuma ga halin da suka samu kananan hukumomin a ciki na fama da bashi,” inji shi.

Kwamishinan ya ce ya dauki damarar kawar da bashin kafin Disamban badi, inda ya ce ya ajiye fiye da Naira miliyan 300 wanda idan ya tara wannan kudi da banki ke dauka za a biya su baki daya.

Sai ya ce ba don asusun hadaka tsakanin Gwamnatin Jihar da kananan hukumomi ba, ba yadda za a yi wasu kananan hukumomin su iya biyan albashi.

Ya ce wadannan matsaloli ba su hana gwamnatin gudanar da ayyukan kyautata rayuwar al’umma a kananan hukumomin ba, inda ya ce a yanzu haka ana ayyukan hanya a kananan hukumomin Darazo da Misau, wato hanyar Sade zuwa Akuyam  da hanyar Burga zuwa Yalwan Mainamaji da wasu hanyoyi a masarautun Bauchi da Katagum. Kuma ma’aikatar ta biya kudin kason jiha da ya kamata a biya asusun Hukumar Ilimin Bai-Daya (UBEC) Naira biliyan daya da rabi inda yanzu haka ake kan gudanar da ayyukan gyare-gyaren makarantun a duk fadin jihar.

Sai da da Aminiya ta tuntubi  tsohon Shugaban Riko na Karamar Hukumar Bauchi, Alhaji Chindo Abdu kan wannan bashi, ya ce kalaman da Kwamishinan ya yi kalamai ne na siyasa. Ya ce  abin da ya faru wannan bashi na Naira biliyan uku shi ne lokacin da gwamnatin ta zo ta samu kananan hukumomi suna wahalar biyan albashi kuma idan an je karbo kaso daga Asusun Tarayya wani lokaci sai a yi ta ka-ce-na-ce, kudin ba sa zuwa da wuri da hakan ke jawo jinkirin biyan albashi, ya sa gwamnati ta yi tsari da banki cewa idan lokacin albashi ya yi ya rika bada kudi ana biya idan kudin kananan hukumomi ya zo sai bankin ya cire kudinsa. “Ta haka ne muka samu hanyar biyan albashi cikin sauki,” inji shi.

Chindo ya ce da bai kamata a yi kalamai don bata wata gwamnati ba, ya kamata ne idan gwamnati ta zo ta ga ita ba ta da sha’awar abin da wancan gwamnatin ta yi sai ta sauya ta dauki nata.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Bauchi Alhaji Kawuwa Shehu Damina, don karin bayanni abin ya ci tura, amma wani tsohon dan majalisa da ba ya so a ambaci sunansa ya ce lokacin da za su yi wannan bashi, sun kawo batun yin yarjejeniyar kuma majalisar ta amince musu, inda ya ce dama ba kasafai gwamnati ke kawo bukata su ki amincewa da shi ba.