✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan rikicin Hausawa da Yarbawa: Gwamnan Oyo ya bude kasuwar Bodija

A shekaranjiya Laraba ce Gwamnan Jihar Oyo Cif Abiola Ajimobi ya bayar da umarnin a bude Kasuwar Bodija wadda aka rufe ta sakamakon kaurewar fada…

Wani bangare na kayan Hauswa da aka lalata a  Kasuwar BodijaA shekaranjiya Laraba ce Gwamnan Jihar Oyo Cif Abiola Ajimobi ya bayar da umarnin a bude Kasuwar Bodija wadda aka rufe ta sakamakon kaurewar fada a tsakanin Yarbawa da Hausawa da ke kasuwancin wake a kasuwar a ranar Juma’ar da ta gabata.
Gwamnan wanda yake tare da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Mohammed Indabawa da manyan jami’an gwamnatin jihar ya roki daruruwan ’yan kasuwar Yarbawa da Hausawa su yafe wa juna su ci gaba da kyautata dangantaka a tsakaninsu.
Ya ce gwamnatinsa za ta ba da tallafin Naira miliyan 30 ga iyalan ’yan kasuwar 14 da aka kashe a Maiduguri. Kuma ya ce ’yan kasuwar da aka lalata kayansu a fadar kasuwar Bodija gwamnain za ta tallafa musu da wani abu, sai dai bai fadi ko nawa ne ba.
Gwamna Ajomobi ya tunatar da ’yan kasuwar cewa “Dukkanmu Yarbawa da Hausawa da Ibo da sauran kabilun kasar nan ’yan Najeriya da za a rika samun rashin fahimta a tsakaninmu, amma wajibi ne mu koyi yafe wa juna, domin dan halas ba ya abu a cikinsa yana yafe duk cutar da aka yi masa.”
A yammacin ranar Juma’ar da ta gabata ne fada ya kaure a tsakanin ’yan kasuwa Yarbawa da takwarorinsu Hausawa da ke harkar sayar da wake a babbar kasuwar Bodija, Ibadan, inda aka farfasa shaguna da manyan motoci dauke da buhunan kayan abinci mallakar Hausawan.
An ce wasu ’yan kasuwa Yarbawa sun yi yunkurin korar Hausawa masu sayar da wake daga kasuwar, sai dai hanzarta aikewa da daruruwan ’yan sandan kwantar da tarzoma da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo Muhammed Abdulkadir Indabawa wanda ya jagorance su da kansa ne ya hana kazantar al’amarin. Jami’an tsaro dauke da bindigogi da motocin ruwan zafi sun hanzarta kwantar da rikicin tare da kare Hausawan inda aka kwashe su cikin motocin safa-safa zuwa unguwanninsu a garin Ibadan.
Kafin fadan sai da Kwamishinan ’Yan sandan ya gayyaci shugabannin bangarori biyu zuwa ofishinsa inda ya sulhunta su, amma bangare daya ya yi biris da shawarwarin da aka ba su domin zama lafiya.  
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa yayin da wasu tsagerun Yarbawa suke kokarin kutsa kai cikin shagunan Hausawa suna dukansu da kulake da sanduna da kananan makamai, su kuma Hausawan fadan ceton rai suka rika yi.
Daga cikin wadanda suka samu raunuka a fadan har da Sarkin Hausawan Bodija Alhaji Isyaka Bazamfare, wanda yana daga cikin masu sayar da wake a kasuwar.
Daga bisani shugaban karamar Hukumar Ibadan ta Arewa, Mista Idris Lapade, ya ziyarci kasuwar inda ya ba da umarnin rufe ta sai illa masha Allahu.
Daya daga cikin motocin da aka lalata a Kasuwar BodijaA jawabinsa ga ’yan jarida Mista Idris Lapade, ya nuna takaici kan aukuwar al’amarin, inda ya ce matakin farko da suka fara dauka domin shawo kan rikicin, shi ne rufe kasuwar da hanzarta gayyatar hukumomin tsaro tare da kwashe ’yan kasuwar zuwa unguwanninsu. “Mun dauki wannan mataki ne domin kwantar da hankalin jama’a da samo hanyar da za a ci gaba da zama lafiya a cikin kasuwar wadda mallakar karamar hukumarmu ce,” inji shi. Ya ce, “babu wanda ya mallaki kasuwar, sai hukuma.”
Kakakin hadaddiyar kungiyar masu sayar da kayan abinci reshen Kasuwar Bodija, Mista Hakeem Emiola, wanda ya kasa fadin dalilin aukuwar rikicin, ya ce yana kyautata zaton fadan ba zai rasa nasaba da irin yadda ake ganin Hausawa suna shigo da wake daga Arewa maso Gabas cikin kasuwar ta Bodija ba, alhali ’yan uwansu Yarbawa sun dakata da fataucin waken. “Wannan ne ya kai mu ga zama da Kwamishinan ’Yan sanda a ranar inda kowane bangare ya amince a rika raba daidai na irin wannan wake a tsakaninsu,” inji shi.
Wata majiya da ta nemi a sakaya ta, ta shaida wa wakilinmu cewa, “bangaren mu Yarbawa na ’yan kasuwar ba mu girmama Kwamishinan ’Yan sanda ba, wannan abin kunya ne gare mu bayan mun amince da sulhu daga baya a same mu da kokarin tayar da zaune-tsaye. Ya kamata mahukunta su dauki matakin shawo kan matsalar.”   
Binciken wakilinmu ya gano cewa, barazanar daukar fansa da ’yan kasuwa Yarbawa suka yi, ta faro ne a watan Mayun da ya wuce lokacin da ’yan fashi suka kashe musu fiye da mutum 10 da kwace musu miliyoyin kudi lokacin da suka je sayen wake a Jihar Borno. A cikin watan Yuni ma an samu aukuwar irin haka a yankin Jihar Borno, inda wasu Yarbawa daga Kasuwar Bodija suka rasa rayukansu da dimbin kudin da suka je sayen waken mai suna (oloyin) da ake rububinsa a Kudu maso Yamma.
Tun a wancan lokuta ne Gwamna Jihar Oyo Abiola Ajimobi, ya ba da umarnin kwaso gawarwakin mamatan daga Jihar Borno zuwa Ibadan inda aka yi musu jana’iza tare da binne su a garuruwansu. Gwamnan, ya yi alkawarin ba da tallafin kudi ga iyalan mamatan da aka ’yan fashi ko ’yan Boko Haram ne suka yi musu yankan rago a lokuta daban-daban.
Bincike ya gano cewa, a yayin da Yarbawan suke zaman juyayin rashin ’yan uwansu da dakatar da fataucin waken, sai suka rika ganin irin waken Hausawa na shigo da shi kasuwar suna sayarwa da tsada. Wannan ne ya haifar da zargin da Yarbawan suka ga Hausawa cewa da saninsu aka kashe musu ’yan uwa domin su mamaye cinikin waken a kasuwar. A dalilin haka ne suka fara yunkurin korar Hausawa daga kasuwar tare da barazanar daukar fansa.
Shugaban Kungiyar Fataken Wake ta Kasa, Alhaji Bala KanoDa yake mayar da martani kan batun Shugaban kungiyar Fataken Wake ta kasa, Alhaji Bala Ahmed Kano, ya yi watsi da zargin da Yarbawan suka yi cewa Hausawa suna bi ta bayan gida suna fataucin waken sun kyale Yarbawa a gefe daya. Ya ce, “Wannan zargi babu kanshin gaskiya a ciki kuma kokarin korar Hausawa daga kasuwar Bodija ne, sannan wata alama ce ta nuna kabilanci da wasu tsiraru daga cikinsu ke son bata dadaddiyar dangantaka da ke tsakaninmu da su. Tun kisan farko da aka yi wa mutanensu a Jihar Borno, mun zauna da su da jami’an tsaro inda su da kansu suka shawarci Yarbawa masu zuwa Borno sayo wake su daina shiga lungunan jihar, su tsaya a cikin garin Maiduguri kawai, amma ba su yi aiki da shawarar ba. Kuma kowa ya san irin halin da ake ciki a Arewa maso Gabas, babu maganar Bahaushe ko Ibo ko Bayarabe kowa tsautsayi na iya rutsawa da shi.”
Alhaji Bala Kano, ya ce, mahukunta sun shaida musu cewa, abin da suke so a yi na dakatar da kawo nau’in waken daga jihohin Borno da Yobe ba zai yiwu ba, domin babu dokar da ta yi wannan tanadi a Najeriya. “Saboda haka, mu a matsayinmu na shugabannin wannan kungiya bangaren Hausawa, ba za mu taba goyon bayan dakatar da sayo waken daga Arewa ba domin yin hakan babban kuskure ne. Kuma har yanzu muna kan wannan matsayi namu. Kuma, ina tabbatar wa duniya cewa, mu a kowane lokaci masu biyayya ne ga dokokin kasarmu,” inji shi.
Dangane da zargin hannun kungiyarsu a kan kisan gillar da aka yi wa ’yan kasuwa 14 a lokuta daban-daban a jihohin Borno da Yobe, sai Alhaji Bala Kano, ya ce, wannan zargi karya ne, domin daga cikin masu zargin babu wanda zai iya fitowa da shaida a kan aukuwar haka. Ya ce yawancin mutanensu da suka dade suna hulda da Arewa sun yi tir da wadannan kalamai marasa tushe.
Sarkin Hausawan Bodija, Alhaji Isyaka Bazamfare, wanda ya tsallake rijiya da baya a fadan“Abin da ya faru a ranar Juma’a, ko kusa ba su kyauta mana ba, domin an yi zaman sulhu da mu da su a gaban Kwamishinan ’Yan sanda mun amince wa juna amma suka tayar da kayar baya suka yi mana barnar kayan abinci da manyan motoci da sauransu, inda muka kiyasta barnar ta kai ta kusan Naira miliyan 30, bayan raunuka da suka yi mana da ya shafi Sarkinmu wanda muke ganin yin haka, shi ne karshen wulakanta mu da kokarin kaskantar da mu ba tare da laifin komai ba. Ya kamata mahukunta su yi wa lamarin tufkar hanci,” inji Shugaban Fataken Waken.