Search
Subscribe
Bayanin Wasan Kwaikwayon Hausa (1)

Marigayi Alhaji Kasimu Yero daya daga cikin fitattun ’yan wasan Kwaikwayon Hausa

Bayanin Wasan Kwaikwayon Hausa (1)

Ma’anar Wasan Kwaikwayo a Hausa a bayyane take daga lura da kalmomin da suka gina shi, wato abu ne mai alamun wasa da kuma kwaikwayo. Shi dai wasa yana nufin duk abin da ba gaskiya ba ne, yana kuma dauke da raha da ban-dariya da nishadi, akwai kuma kwaikwayo, wanda ke nuni da aikata wanin abu don kwatanta yadda yake, ko yadda ake yin sa, ko wajen nuna  kyansa ko kuma muninsa. Abin la’akari a nan shi ne, za a ga cewa wasan kwaikwayo a Hausa ba kamarsu daya da drama a Ingilishi ba, domin su Turawa sun dauki drama ko wasan kwaikwayo a matsayin wata basira da za a shirya a rubuce ta fuskar zube ko waka, mai nuni da yadda rayuwa take gudana ko halayen wadansu, ta hanyar fadi-in-fada da alamtarwa, an kuma fi gudanar da shi a dandali. Duk da cewa akwai ’yar tazara tsakanin wasan kwaikwayon Hausa da yadda yake a cikin Ingilishi, za a fahimci cewa abubuwan nan da Hausawa suka fi mayar da hankali a kai wajen gane wannan abu, suna nan rakube a cikin dukkan wani wasa mai kama da haka a kowane harshe ko al’ada ta duniya. Yaya wasa yake a cikin wasan kwaikwayo, shi kuma kwaikwayo yaya ya kasance? Duk irin wasan kwaikwayo na gargajiya da ka yi nazarin kayan cikinsa za ka ga alamun nan biyu na wasa da kwaikwayo a cikinsa. Misali: Wasan Langa, Wasan ’Yar tsana, Wasan Kalankuwa ko Wasan Marafa (a rubuce). Dangane da haka duk wani tsarin wasa da aka sa gaba idan bai da wadannan siffofi to ba wasan kwaikwayo ba ne. Haka kuma dole ya kasance da wadannan kamanni.

  1. Sake kama ko canja tufafi ko murya.
  2. A samu wani wuri na musamman (wato dandali ko dandamali).
  3. Ya kasance yana dauke da wani sako.
  4. Dole a samu tanka-in-tanka

Mun ciro wannan rubutu ne daga shafin MakarantarMalamBambadiya: bambadiya.blogsport.com

Za mu ci gaba

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin