Bazamfariya

Allah cikin ikonSa Ya jarrabi al’umma, musamman Jihar Zamfara da ibtila’in ’yan bindiga masu ta’addancin garkuwa da mutane don kudin fansa, wadanda kuma suke kashewa tare da kona gidaje da dukiyoyin al’umma.  DOKTA ALIYU U. TILDE ya yi alhinin wannan al’amari, inda ya gabatar da wannan wake nasa mai taken “Bazamfariya.”

Ta’ala mun kira ka,

Gida Naija da Makka,

Na bene har na bukka,

Yakini babu shakka,

ADVERTISEMENT

Ga komi kai iyawa.

 

Ka shaida mun bara’a,

Ga duk wani mun yi a’a,

A saɓo ba mu ɗa’a,

Muna roƙonKa sa’a,

Gabanin mui cikawa.

 

Tsaro yau yai gazawa,

A Hausa da tausayawa,

A kullum ba lafawa,

Da yaɗon ɗan kabewa,

Da sauri ba tsayawa.

 

A Zamfara anka fara,

Abin sanda da gora,

Ya ƙarfafa babu lura,

Da iska har da ƙura,

Ya kai kan Sakkwatawa.

 

Ƙasar Gandi da Isa,

Da ke da natso da hirsa,

A yau an tashi rusa,

Ginin Usumanu ƙusa,

Da Gwamna Bafarawa.

 

Suna nan yammacinmu,

A Birnin Gwari namu,

Zubairu yana kiranmu,

Mu kai ɗauki dukkanmu,

Da sauri ba tsayawa.

 

Kasar Dikko ya jawo,

Ta’adda na ta yawo,

A ɗauke mutum a kawo,

Kuɗaɗe kan ya dawo,

Ga dangi ba ragawa.

 

A Daura sunka sabka,

Magaji yana a garka,

Da ƙarfi sunka ɗauka,

Ya sa Sarki ya koka,

A tashi a zam kulawa.

 

Bare hanyar Abuja,

Farin kaya da soja,

Da manya duk a danja,

A tsorace babu ko ja,

A jirgi za su zowa.

 

Muhammadu sai ka miƙe,

Ka ɗau ɗamara ka tamke,

Da R.P.G. da sulke,

Ta’adda duk ka banke,

Ka himmata ba gazawa.

 

Nasiha ce na ba shi,

Da A’i uwargidanshi

Su ɗau kibiya da mashi,

A kullum babu fashi,

Ka dage gun matsawa.

 

Burutai kar ka zauna,

Ka ɗauki igwa ka auna,

Ga tungar masu ɓarna,

Ka watse duk ka ƙona,

Su tuba su bar mayawa.

 

Sa’an nan ga Sadiƙu,

Yana ta jiran kiranku,

Ya ɗau jirgi ya bi ku,

Ya ba ku tsaro samanku,

Da bom ba dakatawa.

 

Na bi ku ina kirari,

Ina baiti da sauri,

Kumama babu ƙwari,

Da daji ya yi ƙauri,

Na kwanta ban ɗagawa.

 

Da malammai a baya,

Tsayayyu masu raya,

Dare duka ba ritaya,

Da farko har nihaya,

Ijaba sui biɗowa.

 

Arewa ina kiranmu,

Mu taru a dunƙulenmu,

Mu nemi tsaron ƙasarmu,

Amana har da ilmu,

Sana’a sai yabawa.

 

Talauci bai yi kyau ba,

Yana kawo musiba,

Da kunci ga anoba,

Da jari babu riba,

Kasa duk tai macewa.

 

Talauci in ya zauna,

Da kafirci da ɓarna,

Suna biye ba lumana,

Ɗabi’u duk su ƙona,

Mutunci yai ficewa.

 

Kalau muke ko husuma,

A jaki ko a Homa,

Idan an ce mu koma,

Ka sa mu tuna da Kalma,

Mu yi ta wajen cikawa.

 

Salamatun da tsira,

Ga Annabi sa ka ƙara,

Iyaye duk ka tara,

A haula har mu dara,

Dawaman ba gushewa.

 

Da tammat zan tiƙe ta,

Bazamfariya kiran ta,

Watan azumi na yi ta,

Da fuska biyu gare ta,

Wajen mai bincikawa.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya