✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Benezuela: Shugaban ’yan adawa ya bukaci mutanen kasar su ci gaba da zanga-zanga

Madugun ’yan adawa na kasar Benezuela kuma Shugaban Majalisar Dokoki da ya ayyana kansa a matsayin Shugaban Kasa, Juan Guaido ya dawo kasar bayan barin…

Madugun ’yan adawa na kasar Benezuela kuma Shugaban Majalisar Dokoki da ya ayyana kansa a matsayin Shugaban Kasa, Juan Guaido ya dawo kasar bayan barin kasar da ya yi a ranar 23 ga Fabrairu inda ya bukaci a ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati.

A ranar 23 ga Fabrairu Guaido ya tafi kasar Kolombiya domin neman hanyar da za a kawo tallafi da kayayyakin jin kai zuwa Benezuela.

Bayan ya kammala ziyartar Kolombiya, Guaido ya wuce zuwa kasashen Barazil da Paraguay da Ajentina da Ecuador.

Guaido bai yarda da halaccin shugabancin Nicolas Maduro ba, kuma yana samun goyon baya daga Amurka da wasu kasashen Turai da na yankin Latin Amurka da dama.

Da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa a lokacin da ya isa filin jirgin Maikuetia, ya tabbatar wa masu adawa cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da adalci a kasar.

“An riga an fara gwagwarmayar nan, kuma ba zai yiwu mu yi kasa a gwiwa ba. Ba a yin abubuwa yadda suka dace a kasar nan,” inji Guaido.

Guaido ya kara da cewa ya kamata dukan magoya bayansa su tattaro mutane domin ci gaba da zanga-zanga gobe Asabar domin a cewarsa, “Dukkan goyon bayan da muke bukata zai ta’allaka ne da irin dogewarmu wadda watakila za ta hada da zamanmu a kan titunan kasar nan.”