Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Bikin Sallah: Ado Gwanja ya gwangwaje jama’ar jihar Legas

Ado Gwanja

Bikin Sallah: Ado Gwanja ya gwangwaje jama’ar jihar Legas

A ci gaba da bukukuwan Babbar Sallah a jihar Legas shahararran mawakin hausan nan kuma dan wasa Ado Gwanja ne ya gwangwaje al’ummar jihar Legas a harabar gidan radiyon Bond FM da ke Ikeja GRA a yau Asabar.

Mawaka da dama ne suka taya Ado Gwanja, cashewa yawancinsu daga jihar Legas ciki har da Sarauniyar Hamada Falaq Al’amin da babban mai masaukin su B Meri Aboki tare da Bello bokal Manajan Ado Gwanja.

Jama’ar Legas mazan su da mata sunyi yi tururuwa domin kashe kwarkwatar idanun su.

Sauran mawakan da suka cashe sun hadar da Sarauniyar Hamada falaq Al’ameen da B Meri Aboki da sauran su.