Da Dumi Dumi

Bincike: Yadda kananan ’yan mata ke kwarara birane karuwanci

Bincike: Yadda kananan ’yan mata ke kwarara birane karuwanci

Lura da yadda ’yan mata masu karancin shekaru suke fantsama cikin manyan birane a kasar nan don yi karuwanci inda wadansu ke karuwancin kai-tsaye, wadansu kuma su fake da wasu sana’o’i, kamar dirama ko rawar solo yayin da wadansu ma suke karuwancin a gaban iyayensu. Aminiya ta gudanar da bincike na musamman a kan meke haddasa wannan al’amari? Wace riba ko akasi suke samu? Kuma wadanne hadurra suke gamuwa da su a yayin wannan rayuwa tasu? Wakilanmu sun binciko yadda abubuwa suke a wasu daga cikin manyan biranenmu kamar haka:

 Jihar Kaduna:

A Jihar Kaduna, wakilinmu ya gano cewa sana’ar karuwanci tana neman zama ruwan-dare a tsakanin ’yan mata masu kananan shekaru a wasu unguwanni da ke a tsakiyar garin Kaduna. Yawancin ’yan matan da suka tsinci kansu a cikin karuwanci shekarunsu ba su wuce 16 zuwa 20 ba. Kuma akasarinsu suna zaune ne a gidajen iyayensu, kodayake akwai wadanda suka fito daga wasu jihohi suka zo Kaduna domin yawon duniya.

Yawancin ’yan matan suna alakanta dalilinsu na shiga bariki ne da rashin kulawa daga iyayensu, wadansu kuma sukan ce akwai son kai da kuma auren dole da ake yi musu. Binciken da Aminiya ta gudanar ta fahimci cewa wadansu daga cikin ’yan matan da suke sana’ar karuwancin sun fito ne daga unguwannin Rigasa da Tudun Wada da Kawo da Nasarawa da Badarawa da sauransu. Akwai kuma wadanda suka fito daga jihohin Jigawa da Neja da sauransu.

Wadansu sun baro gidajen iyayensu ne suka shigo jihar, inda suka kama dakuna a otel-otel suna holewarsu. Wakilinmu ya gano cewa ’yan matan suna haduwa da mazan ne a gidajen dirama ko na dambe da ke garin, inda wadansu kuma kiransu ake yi a waya su hada su da mazan.

ADVERTISEMENT

Akwai kuma wadansu da kawalai matasa maza  da suke hada su da maza, inda su kuma kawalan ake ba su la’ada. Binciken ya nuna cewa mafiya yawan ’yan matan ana biyansu ne daga Naira dubu uku zuwa Naira dubu goma. ’Yan matan suna kuma kama dakuna ne a otel a wasu unguwanni, inda suke haduwa da mazan su yi lalata.

Wakilinmu ya samu zantawa da wadansu daga cikin ’yan matan a gidan dambe da ke bayan Kasuwar ’Yan Doya a kusa da Kasuwar Ceceniya da ke Kaduna, bisa da sharadin ba za a ambaci sunayensu ba.

Daya daga cikinsu ’yar shekara 16 , ta ce tana zaune a Unguwar Rigasa. Ta ce ra’ayinta ne ya sa ta shiga wannan harka, domin babu wanda ya matsa mata. Ta kuma bayyana cewa ita tana zuwa gidan dambe ko gidan dirama ne domin ta huta, ta yi sha’aninta; idan dare ya yi ta koma gida.

A cewarta, tana komawa gidan iyayenta ne da ke Rigasa da misalin karfe 9 zuwa 10 na dare, duk da cewa ba su san idan take zuwa ba idan ta fita. “Ni dai ba su san ina zuwa gidan dambe ba, domin da farko gidan dirama nake zuwa in yi sha’anina, idan karfe 9 ta yi zuwa 10, in koma gida,” inji ta.

Da aka tambaye ta wane irin sha’ani take yi, sai ta ce “In ga samarina da kuma sauran mutanen arziki ko harka.” Ta kuma ce abin da ke sa ta zuwa gidan damben shi ne, domin ta sha taba, inda ta kara da cewa takan shanye kwali daya a rana, sai dai ita ba ta shan abin da zai sanya ta maye.

An tambaye ta cewa ko mazan da take hulda da su suna cin zarafinsu? Sai ta ce, “Duk macen da namiji ya ci zarafinta sai dai idan ita ta raina kanta,”

Game da batun aure kuwa sai ta ce, “Aure nufin Allah ne, domin Allah ne ke kaddara wa mace yin yawo, wata macen a wajen yawo suke haduwa da mijin aure.”

Ita ma wata budurwa ’yar shekara 19, wacce ta fito daga Karamar Hukumar Turaki a Jihar Neja, bayan aurenta ya mutu ta bayyana dalilinta na shiga karuwanci. Ta ce bayan auren da aka yi mata a shekarar 2015 ya mutu ne ta fito yawon duniya, duk kuwa da cewa iyayenta na can kuma tana ziyartarsu lokaci-lokaci. Sai dai a yanzu ta ce tana zaune da kawayenta ne a wani otel da suka kama daki suna zaman kansu a Kaduna.

“Ni ba na shan taba ko giya. Ba zan yi maka karyar cewa ba na saduwa da maza ba, domin ko na yi maka karya, ai ba zan yi wa Allah ba,” inji ta.

Da aka tambaye ta ko nawa take samu a rana a karuwancin, sai ta ce “Muna biyan daki ne a rana amma ni ban dauki abin a matsayin sana’a ba. Sai dai kurum idan abin ya zo kurum.”

Da aka tambaye ta cewa ko mazan da suke mu’amala da su suna amfani da kwaroron roba saboda gudun cuta? Sai ta ce “Idan mutum na so ba zan hana shi ba, idan kuma ba ya so, babu damuwa.”

Me zai hana ta koma gida, ta bar wannan sana’a? Sai ta ce, “Zan so in koma saboda a kullum ba na jin dadin irin rayuwar da nake yi. Ina kuma addu’a Allah Ya fitar da ni daga cikinta.”

Wata kuma ta bayyana sunanta da Habiba, ta ce ta shigo Kaduna ne saboda kawai ta ji dadin rayuwarta, domin ita Allah Ya yi ta mace mai son jin dadi. Ta ce ita ba ta rayuwar kunci sai dai kurum tana jin tsoron cuta ce kurum.

“Hakan ya sa nake yin addu’o’i a kan Allah Ya raba mu da cuta ko masu yankan kai idan zan bar gida. Amma fa ina shaye-shayen irin su Fakalin da sauransu,” inji ta.

Ko abokan harka nawa take lalata da su a kullum? Ta ce, “Ina iya daukar maza biyu zuwa uku a duk rana, musamman idan na yi shaye-shayena. Kuma babu abin da ke damuna illa kurum inji dadin rayuwata.”

Game da ibada kuwa sai ta ce, “Ni ba na Sallah a kan lokaci, wani lokaci sai na ga dama. Ni fa kurum dadin rayuwata nake son ji.”

Ita kuma wata wacce ta ba da sunanta da A’isha ’Yar Katsina, cewa ta yi “Matsalar kishiyar uwa ce ta jefa ni cikin wannan harka saboda na taso babu uwata a gidan. Har ruwan zafi ta taba watsa mini kuma ta fi karfin mahaifina, baya iya yi mata komai.”

Wakilinmu wanda ya samu ziyartar daya daga cikin gidajen dambe a Kaduna ya kalato cewa akasarin ’yan matan na rayuwar kunci ne a gidajen dambe ko solo, musamman wadanda ba su tare da ’yan daba da ke zuwa irin wadannan gidaje. Bayan haka kuma wadansu ’yan matan na shiga cikin matsala, idan suka ci karo da ’yan-sara-suka ko ’yan daba.

Wakilinmu ya gana da daya daga cikin shugabannin masu zama gidan dambe da ke a bayan Mogadishu, Bala Majaga, wanda ya shawarci ’yan mata su koma gidajen iyayensu kurum su yi aure, domin a cewarsa, irin wannan rayuwa ba ta da amfani.

“Wasunsu na rayuwa cikin jin dadi wadansu kuma na rayuwa ce cikin matsala, domin wata na iya samun abin da ta fito nema wata kuwa ba za ta samu ba.

“Sannan kuma wata matsala da suke fuskanta, ita ce idan jami’an tsaro suka kawo samame, babu ruwansu da ke ’yar daba ce ko a’a. Idan kuma aka kama ki ba ki da kudin belin kanki, sai ki wulakanta,” inji shi.

Bincike ya nuna cewa abu ne mai wahala a iya samun kididdigar ’yan matan da ke shiga harkar karuwanci a jihar ko a irin wadannan gidaje, kasancewar babu jami’i ko wata hukuma da ke daukar kididdigarsu a gidajen.

Wakilinmu ya samu jin ta bakin wani matashi dan shekara 27, wanda yake sana’ar kawalci. Ya kuma shaida masa cewa bai dade da fara sana’ar ba. “Ban wuce wata shida zuwa biyar ba da na fara kawalci, kuma rashin aikin yi ne ya jefa ni nake yi, domin da ina da aikin yi tabbas ba zan yi kawalci ba.

“Na tsinci kaina cikin kawalci ne a lokacin da na fara zama a gaban wani otel a Kaduna. Nakan yi wasa da ’yan matan da ke zama ko zuwa otel din. Hakan ya sa wadansu maza da ke zuwa otel din idan suka gan ni sai su tambaye ni cewa ai sun gan ni da wata yarinya, yaya ake ciki ne? Ni kuma sai in yi mata magana, tunda yawancinsu yawo suke zuwa wajen. Idan na yi musu magana na hada su, ni kuma sai a dauki wani abu a ba ni, haka har na samu wata shida ina aikin,” inji shi.

A kan ko nawa yake samu a kullum sai ya ce “A kullum nakan samu Naira dubu uku zuwa shida a rana amma da yake ba wai ajiye kudi nake yi ba, nakan samu kusan Naira dubu 15 zuwa 20 a karshen wata,” inji shi.

Ko yana kwalcin maza da maza? Sai ya ce “A’a, ni dai mace da namiji kurum nake hadawa ba namiji da namiji ba.” Ya kuma kara da cewa yawancin ’yan matan ba mazauna Kaduna ba ne kadai, wadansu kuma ’yan Kaduna ne.

Kan ko shi ma yana lalata da ’yan matan? Sai ya ce “Ni ba na amfani da su, ni aikina kurum in hada su da maza in samu kudi,” inji shi. A kan ko sana’ar da yake yi tana damunsa

sai ya ce “Tabbas ina samun damuwa a duk lokacin da na je kwanciya ko na sayo abinci ina ci, sai in rika ji a zuciyata cewa wannan fa kudin zina nake ci.” Ya ce muddin ya samu aikin yi zai yi watsi da wannan sana’a ta kawalci.

Limamin Masallacin Titin Faki Road, Ustaz Aminu Abubakar ya ce rashin koyar da yara ilimin addini da kuma rashin tarbiyya daga gida na daga dalilan da ke jefa ’yan matan karuwanci. “Rashin tarbiyya daga gida da rashin karantar da su ilimin addini na daga cikin dalilan da ke jefa ’yan mata cikin wannan mummunar sana’a,” inji shi.

Ya ce karantar da su ilimin addini zai jefa masu tsoron Allah, sannan ya saka masu tausayin iyayensu. Don haka akwai bukatar iyaye su rika bai wa ’ya’yansu ilimi da tarbiyya domin zama nagari a cikin al’umma.

Kwamishinan Ma’aikatar Ci Gaba da Walwalar Al’umma, Hajiya Hafsat Baba ta ce akwai tashin hankali yadda ake samun yawaitar shigar kananan ’yan mata da matasa harkar karuwanci da kawalci a jihar. Ta ce hakika laifin wadansu iyaye ne saboda rashin kulawa da ’ya’yansu ta hanyar tarbiyyantar da su yadda ya kamata.

“Har a ce wai karamar yarinya za ta baro jiharsu zuwa Kaduna ta kama daki a otel tana zaman kanta. Sannan yaro matashi ya rika hada da maza domin a biya shi. Yanzu bincikenmu ya nuna cewa matasan da ’yan mata suna da kungiya ce, ba a Kaduna ba kawai har da wasu jihohi na Arewacin kasar nan.

“Yanzu haka akwai daya daga cikin matasan masu kawalcin ’yan mata da aka kama ya ce har da littafi yake da shi na rubuta sunayen maza da mata, wadanda idan bukatar nemansu ya zo sai dai kurum ya kira.

“A gwamnatance, ba za mu yarda da irin wannan ba, domin otel dai an yi shi ne ya zama inda mutum zai zauna na ’yan kwanaki idan aiki ya kawo shi gari. Amma a yanzu duk kananan otel sun zama inda yara kanana ke zuwa suna zama,” inji ta.

Ta ce yaran kamata ya yi a ce suna makaranta, sannan abin tashin hankali inji ta, shi ne yadda ’yan matan ba su damu da yawaitar cututtukan zamani irin su kanjamau da ke yaduwa a tsakanin al’umma ba. Ta ce gwamnatin jihar za ta yi aiki da masu ruwa-da-tsaki wajen wayar da kan mutane game da hadurran da ke tattare da shiga karuwanci.

Jihar Jigawa:

Yayin da wakilinmu ya ziyarci wani gidan karuwai da ake wa lakabi da Gidan John a garin Dutse a Jihar Jigawa, ya ci karo da matasan karuwan.

Wata mai suna Hussaina Inuwa, ’yar asalin kauyan Gidan Kanta da ke Karamar Hukumar Wudil, ta ce shekararta 23 kuma ta yi aure sau daya, shi ne ta shiga wannan harka; a cewarta saboda mijinta ya rasu. Ta ce sakamakon hakan ya sa ba ta samu wata kulawa da ta kamata a wajen iyayenta ba, shi ne ta fada cikin karuwanci.

Ta ce shekararta uku tana karuwanci kuma ba ta san iya yawan mazan da ta kwanta da su ba daga lokacin da ta fara karuwanci zuwa yanzu.

Bilkisu Ibrahim Jos, wadda ’yar asalin kauyen Shandam ce, ta ce ita ta fara yin harkar karuwancin ce tun kafin ta yi aure.

“Ina cikin karuwancin ne na samu miji na yi aure. Mijina da na aura ya rasu ne, shi ne na sake komowa ruwa. Da na dawo bariki na hadu da maza iri-iri har wata rana wani dadirona ya yi min duka, ya yi min targade guda hudu. Daga nan ’yan sanda suka raba mu, aka shiga tsakanina da shi. Ko yanzu na sami miji zan yi aure,” inji ta.

Ita kuma Fatima Abdu Nasarawa, ’yar asalin kauyen Garegu ce da ke Jihar Nasarawa. Ta ce ita shekararta goma tana karuwanci. “Na taba yin sure kafin in shiga karuwanci. Yau ina da shekara 23 a duniya kuma maza suna sona saboda ban taba haihuwa ba, sai dai ni ban neman maza barkatai. Tsarina maza takwas ne nake hulda da su amma ina satar hanya ina lalata da maza. A wannan fuskar ban san adadin da na kwanta da su ba.

Yayin da ita kuma Maryam Usman Maigatari, ’yar shekara 19, ta ce ita ta taba yin aure, tana da ’ya’ya biyu da ta samu a aure. “Kaddara ce ta sa na shiga karuwanci, ba a son raina ba na shiga karuwanci. Na shiga ne saboda rashin zaman lafiya tsakanina da’ yan uwana saboda haka idan na samu miji zan yi aure. Ko yanzu ba da kowa nake yin harkar ba, akwai iyakacin mazan da na ware nake mu’amala da su.

Ita kuwa Halima Ibrahim, ’yar asalin Jihar Gombe ce, ta ce shekararta 33 a duniya kuma ta yi tsawon shekara10 a cikin wannan harka ta karuwanci. Sai dai a cewarta, “Duk da cewa na jima a wannan harka, zan yi aure. Ban san yawan mazan da na kwanta da su ba, ba za su kirgu ba kuma a kullum ina kwantawa da maza biyar zuwa goma saboda abin da ake ba ni ne nake rayuwa, in ci abinci in sayi sutura, in sayi sabulun wanka da omon wanki da turare. Saboda ita mace ’yar tsabta ce kuma duk da dadewata a wannan harka tsawon shekara goma, ina son wanda yake so na da aure, zan aure shi.”

 Jihar Oyo

A garin Ibadan Jihar Oyo, Aminiya ta ziyarci wani gidan karuwai a Unguwar Ojo, Tudun Wulli (an canja wa unguwar suna zuwa Tudun Sunnah), inda wadansu mata masu zaman kansu da ba su yarda da daukar hotonsu ba, suka yi bayanan dalilin fitowa yawon karuwanci.

Hadiza Muhammed daga Jihar Sakkwato cewa ta yi “Yau shekara 15 ke nan da yi min auren dole, shi ya sa na fito bariki domin iyaye da ’yan uwana sun dage sai sun daura min aure da mutumin da ba na so. Wannan zaman bariki da nake yi babu wani jin dadi sai wahala kawai. A yanzu haka ina yin wata daya ban kula da namiji ba amma na samu rufin asiri a matsayin Magajiya a cikin wannan gida, inda nake lura da dakunan da ake biyan haya.

“A can baya, lokacin da ake harka sosai ina zama da namiji daya ne idan mun kare sai wani ya zo amma ban yarda da hada maza a rana daya ko lokaci daya ba, domin lura da lafiyata. Ai da na kuskura na gwamutsa maza to kuwa da yanzu na ragube, ba zan ganu ba. Iyayena sun san ina nan zaune, ina tuntubarsu a kai-a-kai domin babu jari ne shi ya sa ban koma gida ba,” inji ta.

Rashida Muhammed da ba ta fadi garin da ta fito ba, cewa ta yi “Ina da shekara kusan 14 aka wanke ni, inda na yi shekara 18 tare da mijina muka haifi ’ya’ya 4 amma aurena ya mutu na dawo gidan iyaye ina saye da sayarwa har zuwa lokacin da kaddara ta fito da ni zuwa yawon bariki. Wannan zama da nake yi ban zubar da mutuncina ba, domin kasuwanci nake yi. A kowane wata uku ina komawa gida, domin ganin iyaye da ’yan uwa kuma ina rokon Allah Ya matso min lokaci kusa da zan koma gida kwata-kwata. Su ma sauran mata ina rokon Allah Ya mayar da su gidajen iyayensu lafiya, domin su tuba da wannan kazanta, mu rungumi Sunnar Annabi Muhammadu (SAW).”

“Domin babu alheri a irin wannan zama. Akwai bambancin irin wannan zama da zaman  dakinka da miji domin raya Sunnah. Tunda na fito bariki na fi rungumar sana’a fiye da hulda da maza. Wannan yawon bariki da matasan ’yan mata suke yi babu kyau ko kadan domin kaddara ce da son zuciyarmu da ba ma sauraron gargadin da ake yi mana. Addu’a nake yi a kullum Allah Ya sa mu tuba mu yaki zuciyarmu domin fita daga halin da muke ciki,” inji ta

Ita kuwa Amina Umar daga Lafiyar Barebari a Jihar Nasarawa, cewa ta yi “A gaskiya bakin cikin rayuwa kamar takura da matsi daga iyaye da ’yan uwa ne ya fito da ni yawon bariki. Babu ribar komai a wannan zama da nake yi, sai karin bakin ciki. Ina fatar samun mijin aure domin raya Sunnah. Ina kira ga mahukunta su agaza mana kuma su fadakar da iyayenmu, idan mun yi ba daidai ba su rika zaunar da mu da shawara amma ba tsanarmu ba, abin da ye kara tunzura mu ga yawon bariki.”

Wata yarinya mai suna Binta ’Yar Malam, wacce ta ce daga Kano take, cewa ta yi “Wani saurayina ne ya yi sanadin jefa ni cikin karuwanci ta hanyar koya min shan kayan maye. Ya yaudare ni, ya kai ni Shagamu ya gudu, ya bar ni. Ina iya saduwa da maza 5 a rana wadanda suke biyana  kudi kalilan. Ba zan koma ga iyayena a yanzu ba, domin babu komai a hannuna.”

Wata bebiya kuwa da aka tattauna da ita, cewa ta yi “Matsalar rashin kudi ce ta sa na fito yawon bariki amma idan gwamnati ta taimaka mana da jari to ina tabbatar maka cewa zan bar karuwanci kwata-kwata, in koma ga sana’a.”

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya