✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Birtaniya ta kwace kudin Abacha Naira biliyan 82 na bankin Jersey

An kwace kudin tsohon Shugaban Najeriya Janar Sani Abascha, Naira biliyan 81.9 daga asusun ajiya na bankin Jersey. Shugaban ya mulki Najeriya ne daga shekarar…

An kwace kudin tsohon Shugaban Najeriya Janar Sani Abascha, Naira biliyan 81.9 daga asusun ajiya na bankin Jersey. Shugaban ya mulki Najeriya ne daga shekarar 1993 zuwa 1998 lokacin mulkin soja ya kuma rasu yana mukin kasar.

An bankado wasu hanyoyi da shugaban ya bi wajen karkatar da kudaden daga Amurka. Kafar sadarwa ta UK Metro ta bayyana cewa, an sanya kudaden a asusun ajiya na Bankin Jersey na kamfanin Doraville Properties Corporation, mallakin kamfanin Birtaniya a Virgin Islands.