✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram: Manoma miliyan 1 ba sa iya fita gona a Borno

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya koka da yadda mayakan Boko haram ke jan ra’ayin kananan yara sakamakon fatara da rashin ayyukan yi a jihar.…

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum ya koka da yadda mayakan Boko haram ke jan ra’ayin kananan yara sakamakon fatara da rashin ayyukan yi a jihar.

Furucin Gwamnan ya zo a lokacin da ya ke bayyana kalubalen da ake fuskanta a sansanan ’yan gudun hijira, yayin da ya karbi bakuncin wasu ’yan Majalisar Wakilai da suka kai masa ziyara ranar Alhamis a Maiduguri.

Zulum ya ce, akwai sama da manoma ’yan gudun hijira 700,000 a Monguno da kuma fiye da 400,000 a Gamboru Ngala da ba sa iya zuwa su noma gonakinsu.

Ya ce, zaman dirshan da manoman majiya karfi ke yi a sansanin ’yan gudun hijira ka iya kawo rashin tsaro wanda zai sa matsalolin da ake fuskanta a yanzu su ta’azzara.

“Mafita a nan kawai ita ce mu san yadda za a bi a mayar da wadannan mutanen garuruwansu cikin gata. Amma idan ba haka ba, dole a fuskanci babbar matsala da ta fi wadda muke ciki a yau.”

“Saboda a halin da ake ciki yanzu, mayakan boko haram na jan ra’ayin ’ya’yanmu suna shiga kungiyar sakamakon rashin aikin yi,” inji Zulum.

A rahoton da jaridar The Cable ta wallafa, Gwamnan ya shawarci ’yan majalisar da su mayar da hankali wajen kawo matakai masu dorewa da za su taimaka wajen mayar da ’yan gudun hijira garuruwansu.