✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta kashe Kanar din sojan Najeriya

Mayakan Boko Haram sun kashe Kanar D.C Bako a wata musayar wuta

Mayakan kunigyar Boko Haram sun hallaka mutane da dama a hare-haren da suka kai a sassan Jihar Borno a karshen makon jiya.

A daya daga cikin hare-haren ne mayakan suka kashe wasu sojoji tare da raunata wani mai Kanar DC Bako, wanda daga baya ya rasu a asibiti.

“Abin takaici ne yadda aka rasa dakarun soji ciki har da mai mukamin Kanar wanda ya mutu a asibiti a Maiduguri sakamakon munanan raunuka da ya samu”, inji majiyarmu ta tsaro.

Ta ce an yi musayar wuta ne bayan maharan sun bude wa ayarin motocin sojojin wuta ne a Wajuriko, daura da Sabon Gari a Karamar Hukumar Damboa, su kuma sojojin suka mayar musu da martani.

A musayar wutar ce mayakan na Boko Haram suka harbi Kanar din yayin da wasu sojoji suka kwanta dama.

Majiyarmu ta ce an dauki awanni ana musayar wata da ’yan ta’addan, har sai da karin sojoji suka kai wa takwarorinsu dauki daga Biu da Damboa.

Sojoji sun hallaka da dama daga cikin maharan inda wasu suka tsere da raunin harbin bindiga a jikinsu.

Kakin runduna ta 7 ta Sojin Kasa, Kanar Ado Isa, ya ce dakarun da Kanar D. C Bako ya jagoranta sun hallaka mayakan Boko Haram da dama, inda suka kwato tarin makamai a ranar Lahadi.