✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bude katafaren wajen hutu na Rahama Sadau ya jawo cece-ku-ce

A shekaranjiya Laraba ce fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta bude katafaren wajen hutu mai suna Sadau Home a Kaduna. Wannan wajen hutu, wanda ke kan…

A shekaranjiya Laraba ce fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta bude katafaren wajen hutu mai suna Sadau Home a Kaduna.

Wannan wajen hutu, wanda ke kan Titin Rabah a Unguwar Sarki a Kaduna ya kunshi wajen cin abinci da na wanke kai na mata da wajen aski da wajen shan shisha da sauransu.

Bikin bude wajen ya zo ne kwanakin kadan bayan bikin murnar cikarta shekara 26, wanda bikin ya jawo cece-ku-ce a shafukan sada zumunta, musamman batun bude wajen shan shisha da suturar da ta sanya a wajen bikin.

Malam Muhsin Ibrahim, malami a Jami’ar Cologne ta kasar Jamus, kuma mai sharhi a kan al’amuran da suka shafi Kannywood, ya ce

“Yana da kyau su rika kasuwanci. Duk da cewa zai yi wuya Kannywood ta durkushe baki daya, amma babu tauraron da zai dawwama. Wato idan yau kai ne, gobe ba kai ba ne.”

Da aka tambaye shi batun bude wajen shan shisha, Malam Muhsin cewa ya yi, “To! ya kamata mu gane cewa Rahama ba ta cika damuwa da maganganu ba. Ko dai mu dauki shan shisha a matsayin abu mara kyau, ko abu mai kyau, matukar za a samu riba, shi ke nan. Sannan shan shisha din abu ne na matasan zamani a wurare da dama. Sannan wajen hutun da Rahama Sadau ta bude na matasa ne, ina fata ka gane al’amarin?”

Shi ma wani mai sharhi kuma marubuci a kan Kannywood, Malam Bashir Yahuza Malumfashi ya sanya hoton Rahama Sadau da wani mawaki suna rawa a shafinsa na facebook, inda ya fada cikin azanci cewa, “Bayan na kalli hotunan da idanun basira, babu abin da na tuno sai lokacin da nake yaro karami, lokacin da muka fara kallon fina-finan Indiya. Shekarun da dadewa, can wajajen 1977. Na tuno yadda muke kallon shigar ’yan matan fim din Indiya mu yi musu alkalanci. Ta yaya muke yin haka? Da zarar an hasko fuskar Hema Malini, babu abin da za ka gani sai tsabar kyau da shiga ta kamala da kwalliyar sarka da ’yan hannuwa masu sheki. Don haka a idanuwanmu, ita mutuniyar kirki ce.

A wani bangaren kuma da zarar mun kyalla ido muka ga an hasko Helin shi ke nan, ba tare da raba daya biyu ba, za mu ce ga karuwa. Ba komai ya sanya muke yanke mata wannan danyen hukunci ba sai saboda yanayin shigarta. Babu fim din da za ka ga Helen da suturar mutunci. Haka kuma ba za ka gan ta a gidan afto ko gidan mutunci ba. Ko dai ka ganta a otel tana rawa da waka cikin mayen giya, ko kuma ka gan ta a gidan boss.

“Wannan tunani, shi na yi a lokacin da na ga hotunan Rahma a tare da wani mawaki suna tikar rawa. Sai dai da yake ita ba Bollywood take ba, Kannywood take, ban san irin alkalancin da zan yi mata ba.”