✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budurwa ta banka wa kanta wuta saboda saurayi

A ranar Lahadin da ta gabata ce wata budurwa mai kimanin shekara 17 mai suna A’isha Aminu da ke zaune a Unguwar Albarkawa a garin Gusau…

A ranar Lahadin da ta gabata ce wata budurwa mai kimanin shekara 17 mai suna A’isha Aminu da ke zaune a Unguwar Albarkawa a garin Gusau a Jihar Zamfara ta banka wa kanta wuta saboda saurayinta ba ya da kudin aurenta.

Mahaifin A’isha, Malam Aminu Muhammad wanda aka fi sani da Mai Unguwa ya shaida wa wakilinmu cewa A’isha ta dauki matakin kashe kanta ne bayan ta fahimci cewa saurayinta mai suna Umar ba ya da Naira dubu 17 da zai biya a matsayin sadakin aurenta da aka bukaci ya ba da.

“Mun kira Umar muka ce ya kawo sadaki a daura masa aure da A’isha, to amma sai ya shaida mana cewa ba ya da kudi. Kuma mun fahimci cewa ba ya da wata kwakkwarar sana’a. Yanayin sana’ar acaba, to amma babur din ma ba nasa ba ne. Yana karbar hannun- kwarya ne.

Lokacin da abin ya faru ba na gida na dawo na tarar da ita cikin mawuyacin hali jikinta gaba daya ya kone, fatarta na salewa. Kuma ga shi ba ni da kudi don Naira 750 kacal ke aljihuna,” inji shi.

“Da na ga ba ni da kudi sai na yanke shawarar tsayawa a gida don a yi mata maganin gargajiya don ya fi sauki a gare mu da zuwa asibiti. Muka kira mai maganin gargajiya ya yi mata wasu magunguna koda yake daga baya mun tafi asibitin,” inji shi

Wani makwabcin su A’isha a unguwar ya shaida wa Aminiya yadda lamarin ya faru, inda ya ce lamarin ya ba kowa mamaki saboda A’isha ba ta cika hayaniya ba, kuma ta yi karatun Alkur’ani Mai girma har ta sauka.

“A’isha ta je ta samo fetur ta zuba a jikinta gaba daya sai ta je ta dauko ashana za ta kyasta ta kona kanta. To da yake akwai wata kanwarta a gidan sai kanwar ta yi kokarin hana ta ta hanyar fizge ashanar duk  lokacin da ita A’isha ta yi kokarin kyasta ashanar. Ita kanwar ta A’isha har ta gaji da kokarin hana ta daga baya ta tafi abinta. Daga nan ne A’isha ta kara yin wanka da fetur ta kuma banka wa kanta wuta. Wuta ta kama ta sai ta ruga waje tana ihun neman ceto,” inji shi.

Wani makwabcinsu mai suna Badamasi ya shaida wa wakilinmu yadda suka kashe wa A’isha wutar da ta nemi halaka ta.

“Ina zaune a kofar gida, sai na hango wani bakin hayaki yana tashi sama a gidan, da farko na yi tsammanin babur ce ta kama da wuta can sai na hango yarinya cikin hijabi tana cin wuta kuma duk wanda ta tunkara ya taimake ta sai ya gudu ya ba ta wuri. Daga nan sai na tashi na ruga inda take na tarar da ita tana cin wuta haikan, sai na ruga cikin gida na dauko bokitin ruwa na kwara mata har wutar ta mutu. Da farko na yi tsammanin hadarin gas na girki ne to amma da na tambaye ta abin da ya faru sai ta shaida mini cewa ta yi yunkurin hallaka kanta ne don saurayinta ba ya da kudin aurenta,” inji shi.

Malam Badamasi ya shaida wa Aminiya cewa A’isha ta fada masa cewa da ta je ta rika yin zina saboda rashin aure gara ta kashe kanta.

Malam Badamasi ya ce inda Allah Ya kawo sauki a lamarin da ya iya ganinta bayan ta fito waje. Da ta tsaya cikin gida lokacin da wutar ta kama ta da ta kone gaba daya don babu wanda zai san abin da ke faruwa, saboda lamarin ya faru da safe kowa ya tafi wurin harkokinsa.

Yunkurin wakilinmu na ya samu saurayin na A’isha mai suna Umar ya ci tura saboda bai samu ganinsa ba kuma an shaida wa Aminiya cewa ba ya da waya. Ku ma yana buya ne don kada mutane su dame shi.

To sai dai Aminiya ta samu zantawa da ubangidan Umar mai suna Hassan, ya kuma ce shi saurayin yarinyar ya ce a shirye yake ya auri A’isha duk da halin da ta shiga.

“Shin kansa Umar sai da ya kwanta rashin lafiya saboda tsanani damuwa da abin da ya faru. Lokacin da aka fada masa cewa A’isha ta kona kanta saboda shi, nan take ya yanke jiki ya fadi saboda damuwa. Kuma Umar ya fada min cewa yana son auren A’isha to amma ba ya da kudi,” inji Hassan.

Zuwa yanzu A’isha tana kwance  a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke garin Gusau inda take jinyar raunuka da ta samu sakamakon konewar da ta yi.