✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari da Atiku sun dauki alkawarin amincewa da sakamakon sahihin zabe

A shekaranjiya Laraba ce manyan ’yan takarar Shugaban Kasa Shugaba Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP suka sanya hannu…

A shekaranjiya Laraba ce manyan ’yan takarar Shugaban Kasa Shugaba Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da Alhaji Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP suka sanya hannu a wata yarjejeniyar zaman lafiya kan zaben da za a yi gobe.

Kwamitin Zaman Lafiya na Kasa a karkashin jagorancin tsohon Shugaban Kasa Janar Abdulsalami Abubakar ne ya shirya taron.

’Yan takarar biyu sun yi kira ga ’yan Najeriya su gudanar da zabe cikin lumana da zaman lafiya da kuma kauce wa duk wani rikici ko hargitsi a lokacin zaben.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan Najeriya su yi wa kasarsu addu’a a daidai lokacin da ake fuskantar zaben da kuma kara tabbatar da hadin kai ga ’yan kasar baki daya.

Ya bayyana cewa zabe na da matukar amfani domin yana taimakawa wajen samar da zaman lafiya da shirya kasa ta samu ci gaba, kamar yadda BBC ya rawaito shi yana fada.

A nasa bangaren, Atiku Abubakar ya yi kalamai irin na tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan inda Atikun ya bayyana cewa ba dan Najeriyar da ya kamata ya rasa ransa saboda burinsa na zama Shugaban Kasa.

Wannan ne karo na farko da ’yan takarar suka zauna wuri daya bayan da jam’iyyunsu suka fitar da su a matsayin ’yan takarar shugabancin kasar.

Buhari dai na neman wa’adi na biyune a  karkashin Jam’iyyar APC yayin da Atiku Abubakar wanda ya taba zama Mataimakin Shugaban Kasa ke neman shugabancin kasar a karkashin Jam’iyyar PDP.

Wannan ne karo na biyu da ake sa hannu a kan irin wannan yarjejeniya duk da cewa Atiku bai halarci yarjejeniyar farko da aka yi ba a bara.

Taron sa hannu a yarjejeniyar ya samu halartar tsofaffin shugabannin kasashen Afirka da jakadun kasashe daban-daban da kuma masu sa ido a harkar zabe.

A nasa bangaren, jagoran Kwamitin Abdulsalam Abubakar ya bukaci ’yan siyasar da su sanya kasar a gabansu.

“A matsayinku na shugabannin masu dimbin mabiya, kuna da rawar da za ku iya takawa wajen wanzar da zaman lafiya kamar kuma yadda za ku iya haifar da rikici da rudani a kasar nan. Bai kamaa ku yi abubuwan da za su kara jefa kasar cikin rudani ba. Dole kuma kasance shugabannin nagari,” inji shi.

Abdulsalam ya ce, “Da farko dai zaben ba zai yiwu ba sai da zaman lafiya. Na biyu kuma gudanar da harkokin mulkin ma ba zai yiwu ba sai akwai zaman lafiya a kasa, sannan rashin jituwa a tsakanin jam’iyyu na hana kasa ci gaba. Duk da cewa zabe kamar gasa ce a tsakanin jam’iyyu, a bangaren ciyar da kasa gaba kuwa dole sai sun hada hannu. Dole ne dukanmu mu amince da haka, idan kuma ba haka ba, to lallai babu inda za mu je.”

 

Ba ma goyon kowane dan takara – Amurka da Birtaniya

Amurka da Birtaniya sun ce ba sa goyon bayan kowane dan takara daga cikin masu neman shugabancin Najeriya a zaben da za a yi gobe.

Amurka ta ce tana sanya ido tare da sauran kasashe kan mutanen da ke yin katsalandan a harkokin siyasa, ko kuma suke rura wutar musguna wa ’yan kasa gabanin zaben, ko lokacin da ake yinsa ko bayansa.

Birtaniya kuwa ta ce ’yan Najeriya ne kawai za su iya zabar wanda zai shugabance su, ta hanyar lumana da zabe na gaskiya.

Wata sanarwarar hadin gwiwa da ofisoshin jakadancin Amurka da Birntaniya a Najeriya suka fitar ta ce abin da kasashen biyu suke goyon baya shi ne tsarin dimokuradiyya na gaskiya, da sahihin zabe da za a gudanar cikin zaman lafiya.

Amurka ta ce za ta iya daukar matakan da suka hada da hana shiga Amurka kan duk mutumin da aka samu da hannu a rura wutar rikicin siyasa, ko kuma masu magudin zabe.

Sanarwar ta ce za kuma a iya daukar wannan mataki kan iyalan wanda aka samu da laifi.

Birtaniya ta ce za ta hada kai da kungiyoyin kasashen duniya da wasu kasashen duniya wajen saka ido a zaben na Najeriya.

Sanarwar na zuwa ne kwana daya bayan wasu kafofin watsa labarai sun rawaito cewa Amurka na goyon bayan wani dan takara a zaben da za a yi gobe..