✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari Da Muslim

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi Babi na Biyu: Bayar da daya cikin biyar na ganimar yakin Musulunci yana daga cikin addini: 46. An karbo…

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

Babi na Biyu: Bayar da daya cikin biyar na ganimar yakin Musulunci yana daga cikin addini:

46. An karbo daga Abu Nu’aman ya ce: “Hammadu ya ba mu labari daga Abu Jamrat Duba’iyyu ya ce, na ji Dan Abbas (Allah Ya yarda da su), yana cewa: “Ayarin Abdu Kaisu ya taba zuwa suka ce: “Ya Manzon Allah! Lallai mu kabilar Rabi’atu a tsakaninmu da kai akwai kafiran Mudar ba mu da ikon zuwa gare ka face a cikin watan Almuharram. Ka umarce mu da wasu abubuwar da za mu yi riko da su, mu kira wadanda suke bayanmu da shi.” Sai ya ce: “Ina umartarku da abubuwa hudu, kuma zan hane ku game da abubuwa hudu. Na farko imani da Allah, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Ya kulla yatsarsa da nunin cewa daya. Da tsayar da Sallah bayar da Zakka da azumin Ramadan. Kuma lallai za ku bayar da daya cikin biyar na ganimar yaki. Kuma zan hane ku game da giyar masaki da na akushi da na tukunya da na gora.”

 

Babi na Uku: Bayani game da ciyar da matan Annabi (SAW) bayan rasuwarsa:

47. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abu Zinad daga A’araji daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ba a rabon gadona dinari-dinari. Babu abin da  zan bari face ga ciyarwar iyalaina da masu yi mini aiki, bayan haka dukan abin da  na bari sadaka ne.”

48. An karbo daga Abdullahi Abu Shaiba ya ce: “Abu Usamatu ya ba mu labari ya ce, Hisham ya ba mu labari daga babansa daga A’isha (RA) ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya rasu babu komai cikin dakina wanda rai mai hanta zai ci face rabin mudun sha’ir wanda ke cikin kwanso. Na rika ci tsawon lokaci har ya kare.”

49. An karbo daga Musaddad ya ce: “Yahya ya ba mu labari daga Sufiyan ya ce: Abu Is’hak ya ba ni labari ya ce, na ji Amru dan Haris ya ce: “Annabi (SAW) bai bar komai ba face takwabinsa da farar alfadararsa da wata kasa da ya bar ta sadaka.”

 

Babi na Hudu:

Abin da ya zo cikin bayanin gidajen matan Annabi (SAW) da abin da aka jingina zuwa ga dakunansu. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Ku tabbata cikin dakunanku, kuma kada ku rika fitar banza ta Jahiliyya….” (K:33:33).” Da fadar Allah Madaukaki cewa: “Kada ku shiga gidan Annabi (SAW) face in an yi (ya yi) muku izini…”(K:33:53).”

50. An karbo daga Habban dan Musa da Muhammad sun ce: “Abdullahi ya ba mu labari ya ce, Ma’amar da Yunus sun ba mu labari daga Zuhuri ya ce: “Ubaidullahi dan Abdullahi dan Utbatu dan Mas’ud cewa: Lallai A’isha matar Annabi (SAW) ta ce: “Lokacin da ciwon Annabi (SAW) ya tsananta sai ya nemi izinin matansa bisa ga ya yi jinya a dakina, sai suka yi masa izini.”

51. An karbo daga Dan Abu Maryam ya ce: “Nafi’u ya ba mu labari ya ce, na ji Dan Abu Mulaikatu ya ce: “A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Annabi (SAW) ya rasu a cikin dakina a tsakanin kirjina kusa ga kuncina (haba), kuma Allah Ya hada yawuna (miyau) da yawunsa.” Ta ce, “Abdurrahman ya shigo da Asiwaki lokacin Annabi (SAW) jinyarsa kuma ya yi raunin tauna (asiwaki, sai ya nuna yana son ci) sai na karba na tauna masa, na goge masa baki da shi.”(Wannan shi ne fassarar haduwar yawunta da yawunsa).

52. An karbo daga Sa’id dan Ufair ya ce: “Laisu ya ba ni labari ya ce, Abdurrahman dan Khalid ya ba ni labari daga Dan Shihab daga Aliyu dan Husain cewa: Lallai Safiyyatu matar Annabi (SAW) ta ba shi labari cewa: Lallai ita ta tafi ga Manzon Allah (SAW) domin ta ziyarce shi lokacin da yake I’itikafi a masallaci a goman karshe na Ramadan. Sai ta mike domin ta koma gida, Manzon Allah (SAW) ya mike domin ya yi mata rakiya har sai da suka kai ga kofar masallaci kusa da kofar Umma Salma matar Annabi (AS) sai wadansu mutum biyu daga mutanen Madina suka zo, su za su shude (wuce). Da suka ga Manzon Allah (SAW) sai su ka tafi da sauri. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, musu: Ku komo ku ga ko wace ce tare da ni. Sai suka ce: “Subhanallah ya Manzon Allah! Haka ya yi musu girma, sai Manzon Allah (SAW) ya ce musu: “Lallai shaidan yana isar wa mutum mummunan tunani har ga magudanar jini. Lallai ni na ji tsoron kada ya jefa muku wani abu (tunani) a cikin zukatanku ne.”