Search
Subscribe
Buhari  da Muslim

Buhari da Muslim

Tare da

Sheikh Yunus Is’hak

Almashgool, Bauchi

Babi na Talatin da Biyu:

 

Kulla sulhun zaman lafiya tare da mushirikai bisa wata dukiya da waninta. Da bayanin laifin wanda ya saba wa alkawari. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Idan suka karkata zuwa ga zaman lafiya kai ma ka karba musu…”(K:8:61).

117. An karbo daga Nusaddad ya ce: “Bishiru dan Mufaddal ya ba mu labari ya ce, Yahya ya ba ni labari daga Bishiru dan Yassar daga Sahlu dan Abu Hasmat ya ce: “Abdullahi dan Sahlu ya tafi shi da Muhayyasatu dan Mas’ud dan Zaid zuwa Khaibara lokacin suna cikin sulhu, sai suka rarraba bisa hanya, sai Muhayyasatu ya iske Abdullahi dan Sahlu yana magagin mutuwa cikin jini, da ya mutu ya bisne shi. Da ya iso Madina, sai Abdurrahman dan Sahlu da Muhayyisa da Huwaisatu yaran Mas’ud suka tafi zuwa ga Annabi (SAW). Sai Abdurrahman ya mike zai yi magana sai (Annabi SAW) ya ce: “Bari babba ya yi magana! Bari babba ya yi magana! Saboda shi ne yaro a cikin jama’ar. Da ya yi shiru sauran biyu suka yi magana: (Annabi SAW) ya ce: “Za ku rantse ku cancanci hakkin dan uwanku da aka kashe? Suka ce, “Kamar kaka (yaya) za mu rantse ba mu da shaida, kuma ba mu gani da idonmu ba? Ya ce: “To, Yahudawa za su kare kansu da rantsuwa Hamsin.” Suka ce: “Kaka za mu yarda da rantsuwar kafirai? Sai Annabi (SAW) ya biya diyyar daga wurinsa.”

Babi na Talatin da Uku: Fifikon cika alkawari:

118. An karbo daga Yahya dan Bukair ya ce: “Laisu ya ba mu labari daga Yunus daga Dan Shihab daga Ubaidullahi dan Abdullahi dan Utba cewa: “Lallai Abdullahi dan Abbas ya ba shi labari cewa: Lallai Abu Sufiyan dan Harb ya ba shi labari cewa: Lallai Hirakala ya aika zuwa gare shi lokacin da yake cikin ayarin Kuraishawa a lokacin da suke sulhun barin yaki da Annabi (SAW) ya kulla da Kuraishawa.”

Babi na Talatin da Hudu:

Idan kafirin amana ya yi sihiri za a yafe masa? Dan Wahab ya ce, Yunus ya ba ni labari daga Dan Shihab cewa: An tambaya cewa: Shin kafirin amana idan ya yi sihiri za a kashe shi? Ya ce: “Labari ya isa gare mu cewa: Manzon Allah (SAW) hakika an yi masa haka (sihiri) amma bai kashe wanda ya yi masa haka ba kuma Ahlul Kitab ne.”

119. An karbo daga Muhammad dan Musanna ya ce: “Yahya ya ba mu labari ya ce, Hisham ya ba mu labari ya ce, Babana ya ba ni labari daga A’isha (RA) cewa: Lallai Annabi (SAW) an yi masa sihiri har sai da ya kai yana ganin kamar ya aikata wani abu alhali kuwa bai aikata shi ba.”

Babi na Talatin da Biyar: Abin da aka hana game da yaudara bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Idan sun yi nufin su yaudare ka lallai Allah Ya isar maka kai da  mummunai….”(K:8:62).

120. An karbo daga Humaidiyyu ya ce: “Walidu dan Muslim ya ba mu labari, ya ce, Abdullahi dan Ala’u dan Zaid ya ba mu labari ya ce: Na ji Busra dan Ubaidullahi cewa, lallai shi:Ya ji Abu Idris ya ce: ‘Ya ji Aufu dan Malik ya ce: “Na tafi zuwa ga Annabi (SAW) a lokacin Yakin Tabuka yana cikin wata kubba (lema) ta fata sai ya ce: “Ka lissafa abubuwa shida kafin Sa’ar Kiyama: Na farko dai mutuwata; na biyu cin Baitil Makdisi da yaki; sa’an nan yawan mace-mace wadanda za su same ku, kamar mutuwar garken tumaki; sa’an nan watsuwar dukiya har za a bai wa mutum dinari dari ya doge yana mai fushi (saboda rashin wadatar zuci). Sa’an nan da wata fitina wadda ba za ta rage gidan wani Balarabe ba face ta shige shi. Sa’an nan zaman doya da manja (karamin sulhu) a tsakaninku da Turawa sai su rika yaudara, saboda su zo su yake ku bisa tuta tamanin. karkashin kowace tuta da kamar mayaka dubu goma sha biyu.”

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin