✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na jagorantar taron Majalisar Tsaro

Shugaban Kasa na jagorantar zaman Majalisar Tsaron yayin da zanga-zangar #EndSARS ke gudana

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagorantar zaman Majalisar Tsaro ta Kasa a Fadarsa ta Aso Villa da ke Abuja.

Taron da ke gudana a mako na biyu da ake zanga-zangar #EndSARS ya samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha; da kuma Mai ba da Shawara kan Tsaron Kasa, Babagana Mongun.

Manyan Hafsoshin Tsaro, Shugaban ‘Yan Sanda da na hukumar tsaro ta DSS da Ministocin Harkokin Cikin Gida, ‘Yan Sanda da Kasashen Waje na cikin mahalarta taron.

Manyan Hafsoshin Tsaro a lokacin taron Majalisar Tsaro ta Kasa

Kwana biyu ke nan bayan harbin da sojoji suka yi domin watsa masu zanga-zangar a ranar Talata ta jawo caccaka da ciki da wajen Najeriya.

Kungiyar kare hakki ta Amnesty International da takwarorinta na duniya sun yi tir da harbe-harben da suka ce sun yi sanadiyyar mutuwar mutum 12 a wurare biyu a ranar Talata.

Amma a jawabin da ya yi ranar Laraba, Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce mutum daya ne ya rasu a yamutsin Lekki, wasu 27 kuma suka samu rauni, uku daga cikinsu sun galabaita.

Rundunar sojin Najeriya ta musanta tura dakarunta su watsa masu zanga-zanga duk da cewa wani bidiyo ya nuna sojoji na harbi a iska a wurin da masu zanga-zangar da suka bijire wa dokar kulle a Jihar Legas suka taru.

Buhari da Mashawarcinsa Kan Tsaro, Babagana Monguna a taron.

A ranar Laraba, zanga-zanga ta da fara munana tun a makon jiya ta yi mummunan kazancewa musamman a Jihar Legas inda masu zanga-zangar ta #EndSARS suka kashe ‘yan sanda tare da kona caji ofis akalla guda 10 da sauran gine-ginen gwamnatin jihar da ta tarayya da ma mallakin mutane tare da sace dukiyo.

Tuni dai Majalisar Tarayya ta bukaci Shugaba Buhari da ya yi wa ‘yan kasa jawabi domin shawo kan matsalar.

A nashi bangaren Osinbajo ya bayyana alhininsa game da abin daya faru tare da alkawarin yin adalci ga wadanda abin ya ritsa da su.