✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kaddamar da aikin bututun iskar gas a Arewa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas mai tsawon kilomita 614 a Arewacin Najeriya. Bututun iskar gas din mai suna…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas mai tsawon kilomita 614 a Arewacin Najeriya.

Bututun iskar gas din mai suna AKK zai taso daga Ajaokuta a jihar Kogi, ya biya ta Abuja, zuwa Kaduna, ya karasa zuwa Kano.

Da yake lura da kaddamar da aikin ta fasahar taro na videoconference a ranar Talata daga Fadar Gwamnati a Abuja, Buhari ya ce shimfida bututun abu ne mai muhimmanci ga ‘yan Najeriya, don haka ba za a bari ya lalace ba.

Buhari wanda ya ce aikin zai taimaka wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin Najeriya ya ce wajibi ne a yi dukkan mai yiwuwa wajen aiwatar da aikin yadda aka tsara shi, a kuma kammala shi a kan kari.

An bude aikin ne daga kusurwa biyu, inda Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya wakilci Buhari ta bangaren Ajaokuta tare da Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari.

A daya bangaren Kuma, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna sun kaddamar da aikin daga Rikachikun tare da Karamin Ministan Albarkatun Mai.