✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kaddamar da majalisar wadatar da kasa da abinci

A ranar Litinin da ya gabata ce Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da Hukumar Wadata kasa da Abinci (National Food Security Council). A yayin…

A ranar Litinin da ya gabata ce Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da Hukumar Wadata kasa da Abinci (National Food Security Council).

A yayin da yake kaddamar da hukumar, Shugaba Buhari ya bayyana shekara ukun da gwamnatinsa ta shafe a matsayin masu wahalar gaske a tarihin siyasar kasar nan, yana mai cewa “Najeriya kasa ce da ke cike da bukatar samar da guraben ayyukan yi wadanda shugabannin baya suka yi watsi da haka, amma yanzu mun fuskanci wannan matsala don mai da mafarkin zuwa gaskiya.”

Ya kara da cewa, “Mun kaddamar da wani shiri na musamman a karkashin shirin bunkasa zuba jari na kasa (NSIP), wanda zai mai da hankali wajen inganta rayuwar miliyoyin al’ummar kasar nan da suka shafi noma da sana’o’i da kuma habaka tattalin arzikin kasa a karkara da maraya domin ceto rayuwar miliyoyin al’ummar kasar nan.” .

Hukumar wadda shi da kansa zai shugabanta, ta kunshi mambobin da suka hada da gwamnonin jihohin Kebbi da Taraba da Filato da Legas da Ebonyi da kuma Delta. Akwai kuma wakilan ministoci da ma’aikatun gwamnati masu ruwa- da-tsaki a cikin lamarin. 

Gwamnatin Tarayyar dai ta ce wadannan bangarori biyu suna da damar da za su mika bayanan damuwarsu da shawarwarinsu ga hukumar. Haka zalika sabuwar hukumar za ta kula da batutuwan da suka shafi wadata Najeriya da abinci da samar da karin hanyoyin bunkasa noma da manoma da magance rikicin manoma da makiyaya ta hanyar samar dazukan kiwo da burtaloli da koguna da madatsun ruwa da sauransu.