✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: Ba za mu zura wa mabarnata ido ba —Buhari

Ya yi kashedi ga masu fakewa da suna zanga-zangar #EndSARS suna aikata ta'asa

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa masu zanga-zangar #EndSARS da cewa gwamantinsa ta yi nisa wajen biyan sauran bukatunsu baya ga rushe rundunar ‘yan Sandan SARS da cin zalin da jami’anta ke yi ya haifar da zanga-zagar.

Sai dai kuma ya yi kashedi da cewa gwamnatinsa ba za ta zura ido bata-gari na yin kama karya a kasar ba da sunan zanga-zangar lumana ko yanci.

A jawabinsa ga ‘yan Najeriya bayan kazancewar zanga-zangar da ta kai ga asarar rayuka da dukiyoyi, Shugaban ya ce, “Mun saurara tare da nazarin bukatu biyar na masu zanga-zangar, mun karbe su kuma nan take muka soke SARS tare da daukar matakan biyan sauran bukatun matasan.

“Tun lokacin da aka soke SARS na sanar cewa hakan ya dace da aniyarmu ta yin cikakken garambawul ga aikin dan sanda”.

Game da karin albashin ‘yan sanda da suka bukata, Buhari ya ce, “Na riga na umarci hukumar tasara albashi da ta kammala aiki a kan sabon tsarin albashin jami’an ‘yan sanda”.

Ya yi gargadi ga wadanda ya ce ke ganin saurin daukar matakan da gwamnatinsa ta yi kan matsalar a matsayin rauni domin cimma miyagun manufofinsu.

Kakkausan murya

Da yake magana kan rikidewar zanga-zangar ta #EndSARS zuwa barna, Buhari ya yi kashedi ga masu fakewa da sunan zanga-zangar da ta faro cikin lumana suna kashe-kashe da barnata dukiyoyin gwamnati da na daidaikun jama’a.

Ya ce mutanen da suka rika karkashe mutane, fasa gidajen yari, kai wa jama’a hari, cin zarafi da barnata kadarori ba su wata alaka da zanga-zangar da matasan suka faro cikin lumana.

“Ina bakin cikin cewa an samu asarar rayuka; Sam baba bukatar hakan kuma miyagun ayyukan ba su da wata alaka da manufar matasan kasarmu na bayyana damuwarsu”.

Saboda haka ya yi “gargadi ga bata-garin da suka suka kwace zanga-zangar suka kuma wofitnar da hankulan wadanda suka faroshi cikin lumana.

“‘Yancin ‘yan kasa ne su bayyana damuwarsu ta hanyar zanga-zanga cikin lumana…

“Amma ‘yancin zanga-zangar ya kuma wajabta wa masu zanga-zanga mutunta hakkokin sauran jama’a da kuma yin komai bisa doka”.

Ya ce duk da matakan da gwamnati ta dauka na kyautata rayuwar ‘yan kasa musamman matasa, “kar a sha’afa cewa hakki ne a kanta da ta kare ‘yacin ‘yan kasa na gudanar da harkokinsu ta kuma kare su daga duk wata barazana”.