✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya mika wa Majalisar Dattawa sunan sabon shugaban FIRS

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban Hukumar Tara Haraji ta kasar, FIRS sannan ya aika wa Majalisar Dattijan kasar sunan sabon shugaban domin…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban Hukumar Tara Haraji ta kasar, FIRS sannan ya aika wa Majalisar Dattijan kasar sunan sabon shugaban domin amincewarta

A wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Buhari, Garba Shehu, ya fitar ta ce Buhari ya mika sunan Muhammad M. Nami a matsayin sabon shugaban hukumar FIRS.

Shugaba Buhari ya amince da sababbin mambobin hukumar daraktocin FIRS.

A yau Litinin 9 ga Disamba 2019 wa’adin tsohon shugaban FIRS Tunde Fowler, ya kare sannan an ba shi umarnin mika wasikar aje aiki ga babban Daraktan Hukumar.