✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nada Mele Kyari Babban Manajan NNPC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Mele Kolo Kyari a matsayin sabon Babban Manajan rukunin kamfanin mai na Najeriya, NNPC. A sanarwar da mai magana…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Mele Kolo Kyari a matsayin sabon Babban Manajan rukunin kamfanin mai na Najeriya, NNPC.

A sanarwar da mai magana da yawun kamfanin NNPC, Ndu Ughamadu, ya fitar ta ce Shugaba Buhari ya nada wasu sabbin shugabannin bangarorin kamfanin guda bakwai.

Har zuwa lokacin da aka nada shi sabon babban Manajan NNPC, Mele Kyari shi ne shugaban bangaren harkokin danyen mai na kamfanin NNPC, kuma tun watan Mayun 2018, shi ne wakilin Najeriya a Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC.

Sanarwar ta kara da cewa, a ranar 8 ga watan Yuli na 2019 ne dai sabbin shugabannin za su fara aiki.