✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bukaci damar karbo sabon bashi

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da bukatar karbo sabon bashin Naira biliyan 850 saboda gudanar da wasu aikace-aikace a cikin kasafin kudi na shekarar 2020.…

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da bukatar karbo sabon bashin Naira biliyan 850 saboda gudanar da wasu aikace-aikace a cikin kasafin kudi na shekarar 2020.

Buhari ya mika bukatar hakan ne a wani sako da ya aike wa Majalisar Dattawa wadda shugaban majalisar, Ahmad Lawan, ya karanta a zamanta na ranar Talata.

A sakon, Buhari ya bukaci majalisar ta bai wa gwamnati damar tattaro bashin a cikin gida saboda gudanar da aikace-aikacen.

Sakon dai bai ba da bayani a kan aikace-aikacen da za a gudanar ba.

Shugaban majalisar ya umarci kwamitinta na kudi da ya yi aiki tare da Ministar Kudi saboda samo cikakkun bayanai a kan bashin.