✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya sake sabunta wa’adin Akanta Janar na Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sabunta wa’adin Akanta Janar na Najeriya, AGF, Ahmed Idris. Daraktar watsa labarai ta ofishin shugabar ma’aikatan gwamnati tarayya (OHoSCF), Misis…

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sabunta wa’adin Akanta Janar na Najeriya, AGF, Ahmed Idris. Daraktar watsa labarai ta ofishin shugabar ma’aikatan gwamnati tarayya (OHoSCF), Misis Wunmi Ogunmosunle, ce ta sanar da hakan yau Laraba a Abuja.

A cewar Misis Wunmi, kimanin mako uku kenan da rantsar da shugaban Najeriya a wa’adi na biyu amma ba a nada wasu mukamai. Sakataren Gwamnatin tarayyar Najeriya Mista Boss Mustapha, ne rattaba hannu a takardar sabunta wa’adin Akanta Janar din, wanda zai fara aiki daga ranar 25 ga watan Yuni 2019.