✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya sanya wa kasafin kudin bana hannu

A watan Disambar bara ne, Shugaba Buhari ya gabatar wa da Majalisar Tarayya kasafin kudi na Naira tiriliyan 8.83, sai dai majalisar ta kara Naira biliyan…

A watan Disambar bara ne, Shugaba Buhari ya gabatar wa da Majalisar Tarayya kasafin kudi na Naira tiriliyan 8.83, sai dai majalisar ta kara Naira biliyan 90 da miliyan 300 inda ta amince da kasafin na Naira tiriliyan 8.91.

An tsara kasafin ne bisa hasashen Najeriya za ta fitar da gangar mai miliyan biyu da dubu dari uku a kowace rana.

Har ila yau, an gina kasafin bisa hasashen farashin danyen mai a kan Dala $60 kan kowace ganga, da kuma kan farashin canji Naira 305 a Dala daya.

Idan za a iya tunawa dai Shugaba Buhari ya sha tafi da ihu a majalisa, yayin da yake jawabi kafin gabatar da kasafin kudin na bana.

Shugaban ya ce wannan shi ne jawabin gabatar da kasafin kudi na karshe a Majalisar Tarayya ta takwas.

Wannan ne kuma kasafi na karshe da shugaban ya gabatar a wa’adin mulkinsa na farko da ya kare a ranar Laraba da ta gabata.

A jawabin nasa, Shugaba Buhari ya ce Najeriya ta fita daga koma-bayan tattalin arziki, sannan an samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki, lamarin da ya janyo ma sa sowa da ihu daga bangaren ‘yan adawa a zauren majalisar.

An ji wasu  a majalisar  suna cewa “Karya ne!” yayin da Buhari ke bayyana nasarorin da gwamnatinsa ta samu, wasu kuma na yi masa tafi domin kara masa karfin gwiwa.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa ta yi aiki tukuru wajen samar da hasken wutar lantarki, bunkasa harkar noma, samar da ayyuka da kuma ci gaban al’umma.

Kuma ya ce a kowace jiha akwai aikin hanyoyi da gwamnatinsa ta yi. Ya kara da cewa  an kuma yi kokari wajen taimaka wa jihohi da tallafi, domin biyan albashi da ‘yan fansho. A kasafin kudin na bana, akwai Naira triliyan 2.14 da aka ware domin biyan basussuka.

Kasafin ya zarce na shekarar da ta gabata.