✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya umarci Ministoci da su ci gaba aiki zuwa Talata

A yau Laraba shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Ministocinsa da su ci gaba da aiki har zuwa ranar Talata 28 ga watan Mayu 2019. Shugaban…

A yau Laraba shugaba Muhammadu Buhari ya umarci Ministocinsa da su ci gaba da aiki har zuwa ranar Talata 28 ga watan Mayu 2019. Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin taron majalisar zartarwa ta kasa FEC da aka yi yau.

Shugaba Buhari ya umarci ministocin da su mika takardun ajiye aikinsu ga Sakataren Gwamnatin tarayya Mista Boss Mustapha, ya kuma ce wannan shine taron majalisar na karshe da suka yi da Ministocin.

Shugaban ya gode wa Ministocin wajen gudunmawar da suka bayar a wannan gwamnatin.

A ranar Laraba ta makon gobe 29 ga watan Mayu za a rantsar da Shugaba Buhari a karo na biyu.