Daily Trust Aminiya - Buhari ya yi wa Arewa dodorido – Yahaya Kwande
Subscribe

Ambasada Yahaya Kwande

Buhari ya yi wa Arewa dodorido – Yahaya Kwande

Ambasada Yahaya Kwande tsohon ma’aikacin gwamnati ne da ya yi aiki tun zamanin Gwamnatin Jihar Arewa ta marigayi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, inda ya rike matsayin D.O a garuruwa daban-daban na Arewa. Tsohon dan siyasa ne da ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen tsayar da tsohon Shugaban Kasa marigayi Alhaji Shehu Shagari takara a Jumhuriyya ta Biyu, kuma na hannun damar dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar PDP ne Alhaji Atiku Abubakar a zaben da ya gabata. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana ra’ayinsa kan Gwamnatin Shugaba Buhari, inda ya bayyana cewa shugaban dodorido ya yi wa al’ummar Arewa. Ya kuma tattauna wasu al’amuran da dama, ga yadda ta kasance:

Mene ne tarihin rayuwarka a takaice?

An haife ni ne a garin Kwande da ke Karamar Hukumar Shendam a Jihar Filato a 1929, wato shekara 90 da suka gabata. Iyayena Musulmi ne dukkansu kuma mu kabilar Ankwe ne. A lokacin da na taso, babu wata makaranta ta Musulunci a wannan yanki. Sai dai idan za ka tafi Lafiya ko Awai. Don haka a wannan kauye na Kwande sai aka sanya ni a makarantar Mishan ta Darikar Katolika. A lokacin da nake wannan makaranta, idan na dawo gida ina Musulmi, idan na koma makarantar kuma ina Kirista. Idan na dawo gida sai a ce tashi ka je ka yi Sallah, idan na koma makarantar kuma saboda ni kadai ne Musulmi, sai in fada cikin Kirista. Har ta kai ina taimaka wa Fada na lokacin, wajen gudanar da ayyukan addinin Kirista. Amma daga baya da na ci gaba da karatu, sai Allah Ya fitar da ni.

Daga nan na zo na kama aikin koyarwa, aka tura ni Wase, lokacin Sarkin Wase Alhaji Abdullahi Maikano ya rike ni kamar dansa, ya karfafa mini addinin Musulunci.

Daga nan na zo Kwalejin Horon Malamai ta Toro a Jihar Bauchi. Daga nan na tafi Babbar Kwalejin Koyarwa ta Katsina. A nan na karfafa addinina na Musulunci. A nan na yi aure, na auri ’yar Wazirin Katsina, kanwar Ministan Ilimi na Sardauna, marigayi Alhaji Isah Kaita.

A lokacin mu ne masu dan ilimi saboda akidar Sardauna ta ‘Arewa Sai Dan Arewa’ ya dauke mu saboda ba ya son mu zama bayin wadansu. Don haka ya nada ni D.O aka tura ni Kano, daga nan aka tura ni Kwantagora daga can aka tura ni Borno da Potiskum da Bima da nan Jos. Kuma ni ne na shirya zaben da aka yi a Arewa baki daya, a 1961, lokacin da nake D.O a Kano.

Bayan haka na rike Sakataren Mulki na En’e a lokacin. Daga nan Sardauna ya tura mu Ingila zuwa Jami’ar Odford, don  mu koyo al’amuran tafiyar da mulki. Bayan na dawo na shiga aikin sakatare. Kuma na yi Jakadan Najeriya a kasar Switzerland, zamanin Gwamnatin tsohon Shugaban Kasa, marigayi Alhaji Shehu Shagari.

A matsayinka na tsohon ma’aikacin gwamnati tun zamanin Turawa, yaya za ka kwatanta yanayin aikin gwamnati yake a wancan lokaci da yanzu?

To kowane lokaci yana zuwa da irin nasa tsarin. Wato lokacin da muka karbi mulki daga hannun Turawa, iyayenmu su Sardauna suna da tunanin a yi gaskiya ga talaka. Mu ma ma’aikata mun san cewa muna yi wa talakawa aiki ne. A lokacin idan kana aiki ka san kana da aiki, domin babu wanda zai wayi gari ya kore ka daga aiki gobe, dole sai an bi ka’ida. Amma yanzu Gwamna zai ce kai ne Babban Sakatare, ka hau kan manyan ma’aikatan da suke sama da kai a wurin aiki. A lokacinmu babu irin wannan, don haka akwai bambanci kan yadda ake aikin gwamnati a da da yanzu.

Daga kan Shugaban Kasa na soja, marigayi Janar Murtala aka fara samun rikici a aikin gwamnati, lokacin da aka kori ma’aikata da dama. Kuma tun daga nan cin hanci da rashawa ya fara a aikin gwamnati a Najeriya saboda ma’aikaci yana ganin gobe za a iya korarsa. Amma zamanin da muka yi aikin gwamnati, idan ka yi laifi za a bincike ka. A lokacin an so a kore ni saboda na ki daukar hanya ta zuwa garinmu, na bi doguwar hanya ta Langtang.

A da ana binciken ma’aikata, ba bari ake yi sai ka saci dukiyar gwamnati ka tara za a bincike ka ba. Yanzu sai a bar ka ka yi satar, ka yi mulki ka ji dadin da kake so, sai wata rana a fado maka. Amma a da ma’aikaci yana tsoron ya yi sata, domin a duk karshen shekara akwai odita mai bincike, da zai zo ya binciki ma’aikataci.

Don haka bayan shekara biyu sai odita mai bincike ya zo aka ce na bi hanyar Langtang zuwa Shendam, aka ce na yi niyyar sata ce. Bambancin wannan hanya bai fi mil 30 ba, kudin da za a ba ni duk mil daya kwabo 7 ne daga Minna. Kuma ni na bi waccan hanya ce saboda an yi ruwa a lokacin gada ta karye. A lokacin da kyar na tsira, sai da na samu jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da ta dauki labarin karyewar wannan gada a lokacin na kai sannan na tsira.

Yanzu an zo a kasar nan an rasa inda gaskiya take, domin a da idan za ka yi sata za ka bari sai dare ya yi, sannan ka fito da bakin kaya ka boye ka yi satar. Amma yanzu da rana ma sai ka yi sata, ba tare da ka ji tsoron komai ba. Don haka yanzu a Najeriya an kai wani matsayi mai hadari.

Wane tasiri Arewa take da shi wajen shugabancin kasar nan?

Arewa tana da babban tasiri a shugabancin kasar nan, domin mu ne muka gaji shugabanci tun zamanin Shehu Usman Dan Fodiyo. Misali, lokacin da aka zo za a mayar da mulki ga farar hula a Jumhuriyya ta Biyu, ina cikin mutum biyar-biyar da aka dauko daga kowace jiha a Najeriya; muka hadu da Arewa da Kudu a Legas muka yi taro.

A wajen taron, mutanen Kudu suka ce mana za mu kafa jam’iyya daya don sojoji su tafi. Amma idan mun kafa jam’iyyar, ku mutanen Arewa ku yarda ku ne za ku yi shugabanci. A yankin Yamma ku ba mu shugabancin jam’iyya. Kuma duk wanda aka dauka Shugaban Kasa daga Arewa, ya dauko Mataimaki daga yankin Kudu maso Gabas. Shi ne muka dawo gida muka hadu a Kaduna, don mu zabi wanda zai yi mana takarar shugabancin kasar nan, karkashin Jam’iyyar NPN.

A wajen wannan taro, sai ya zamo kowa ya zabi dan jiharsu. Da aka zo kan mutanen Jihar Filato sai muka zabi Alhaji Shehu Shagari a matsayin wanda zai yi takarar shugabancin kasar nan, karkashin Jam’iyyar NPN. Mu mutane Filato ne muka tsaya wajen ganin an zabi Alhaji Shehu Shagari a matsayin dan takarar Shugaban Kasa a karkashin Jam’iyyar NPN. Kuma sunan wannan jam’iyya na NPN, Malam Aminu Kano ne ya sanya mata, domin da shi aka kafa ta. A wajen raba mukamai ne aka samu matsala da mutanensa, don haka suka fita suka je suka kafa Jam’iyyar PRP.

Don haka kamar yadda a duniya babu yadda za a yi shugabanci ba tare da an tuntubi Ingila ba, haka babu yadda za a yi shugabanci ba tare da Arewa ba a Najeriya. Kuma babu yadda za a yi mulki a Najeriya ba tare da Hausa/Fulani ba. Amma abin takaici yanzu babu shugabanci a Arewa kuma idan aka ce babu shugabanci a Arewa, to babu shugabanci a Najeriya. Don haka dole ne mu mutanen Arewa mu cire son dukiya, mu dawo kan cewa zaman lafiya ya fi kudi a kasar nan. Idan ba mu yi haka ba, ba za a samu zaman lafiya a kasar nan ba.

Wadansu mutanen Arewa suna cewa su ba ’yan Arewa ba ne, don haka babu ruwansu da Arewa, me za ka ce kan masu irin wadannan maganganu?

Ni abin ma yakan ba ni dariya, idan irin wadannan mutane sun ce su ba ’yan Arewa ba ne. To, su mutanen ina ne? Komai kin Bahaushe ga kabilar Birom da Arago da Ankwai kabilata da zarar ka je Kudu za a ce maka Bahaushe ne; domin al’adunmu da rayuwarmu daya ne.

To, yaya kake ganin tafiyar gwamnatin Shugaban Kasa Buhari?

Buhari dodorido ya yi mana a Arewa. Ni na san Buhari tun yana saurayi don ya yi aikin soja da kanena Janar Martin Adamu. Mutum ne kyakkyawa da idan ka gan shi za ka yi sha’awarsa, kuma sai ya dauki wani hali da zai rufe idon mutane.

Misali lokacin da ake cikin wahalar rashin mai a kasar nan. Idan Buhari ya zo shan mai a gidan mai, ya ga layin motoci kamar 200, sai ya tsaya a bayansu. Idan aka ce ranka ya dade shiga gaba a zuba maka, sai ya ki. Ya ce ranar da ke dukanku ita ce za ta doke ni. Ta haka ya rika nuna wa mutane shi mai son gaskiya ne. Da haka ya sayi mutanen kasar nan.

Buhari mutum ne wanda ya nuna yana da gaskiya, don haka ni ma lokacin da aka zabe shi ina tare da shi. Domin na yi tunanin zai gyara kasar nan.

Amma yanzu abin da mutane suke kuka har da ni, mutanen da suke kewaye da Buhari da ’ya’yansu da matansu, duk wanda ka ce yana cin hanci sai a ce maka yana yi. Har dansa da matarsa an zarga.

Amma shi Buhari babu shakka, mun san cewa yana da manufa ta ya gyara kasar nan. Ba mu sani ba ko daga baya ne ya ga wannan manufa tasa ba za ta kai shi ya yi aikinsa ba, dole sai ya tara irin wadannan mutane ba mu sani ba. Matukar Buhari ya ci gaba da barin wadannan mutane wadanda duk Najeriya an san cewa barayi ne, duk wani aiki da zai yi na banza ne.

Farkon zuwan Buhari jin sunansa ma kawai ya hana sata. Daga baya da ’yan Najeriya suka ga abin ba haka ba ne, shi ne wadansu suka fara sabuwar barna a Najeriya, fiye da yadda ya zo ya samu ana yi.

Farkon zuwan Shugaba Buhari ku dattawan Arewa kuna tare da shi amma daga baya sai kuka yi hannun riga, me ya kawo haka?

Na gaya maka cewa ina tare da Buhari lokacin da ya zo, duk da ban yi masa yakin neman zabe ba. Saboda dan takarana shi ne Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar. Amma lokacin da Buhari ya ci zaben fid-da-gwani a

jam’iyya, mun koma mun bayar da goyon bayanmu baki daya gare shi. Domin muna ganin shi ne zai ceto kasar nan. A lokacin mu dattawan Arewa mun je wajensa, mun kai masa rubuce-rubuce kan ga yadda za a yi a Arewa muka ba shi. Muka ce mutanen Kudu suna kinmu, mu mutanen Arewa don haka ka tsaya ka rike Arewar nan da gaskiyar da aka sanka da ita. Ka yi abubuwan da za mu karu da su a Arewa. Ka jawo ruwa daga Kudu zuwa Arewa, domin a rika dauko kayayyaki a jiragen ruwa zuwa Arewa saboda bacin rana. Dan uwanka tsohon Shugaban Kasa marigayi Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa ya fara wannan aiki, don haka ka ci gaba. Amma abin mamaki maimakon ya yi haka sai ya dauki aikin kasar baki daya ya damka wa mutanen Kudu. Ya je ya dauki ayyukan ci gaba na kasar ya bai wa mutum daya dan Kudu.

Don haka ni a ganina Arewa ba ta samu komai ba a Gwamnatin Buhari. Dubi hanyoyin da ake yi daga Legas zuwa Imo. Dubi halin da muke ciki yanzu a Jos. Mu mutanen Filato mu ne aka fi yin watsi da mu a wannan gwamnati ta Buhari. Da gangan wannan gwamnati ta rika nada mana wadanda ba su san abin da ake ciki ba, a cikin Majalisar Zartarwa ta Buhari. Yanzu idan ka fito daga Kaduna zuwa Jos hanyar babu kyau ta lalace babu hanya mai kyau zuwa Jos daga ko’ina.

Mene ne dangantakarka da Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar?

Wato abin da ya sa nake tare da Atiku, ni ban saba da tsalle-tsalle ba. Lokacin da marigayi Sardauna ya kwakwulo ni da taimakon marigayi Alhaji Isah Kaita Wazirin Katsina muna tare da shi har Allah Ya yi masa rasuwa. Bayan haka tun da na tsaya wa marigayi Shugaban Kasa Shehu Shagari haka muka zauna ban bar shi ba, har soja suka kwace mulki. Lokacin da aka zo za a sake mayar da mulki ga farar hula muka nemi marigayi Alhaji Shehu Musa ’Yar’aduwa ya zo ya yi mana takara ya zo har nan Jos. Atiku daga baya ya zo ya hadu da mu muna tare da ’Yar’aduwa. Shehu ’Yar’aduwa ya rasu ya bar shugabancinsa ga Atiku, shi ya sa nake tare da Atiku, in ta baci muna tare idan ta yi kyau muna tare. Domin ina ganin yana da wata niyya ta kyautata wa mutanen Najeriya, musamman ’yan Arewa. Domin yana ganin shi ya taso yana maraya amma yau ga irin daukakar da Allah Ya yi masa a cikin mutanen Arewa. A kullum idan muna magana nakan ji yana maganar ci gaban Arewa da mutanen Arewa don haka nake tare da shi.

texem
More Stories