✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya yi wa Atiku ta’aziyar rasuwar hadiminsa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi  wa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ta’aziyyar rasuwar babban hadiminsa da suka dade tare Alhaji Umar Pariya. Wata…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi  wa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ta’aziyyar rasuwar babban hadiminsa da suka dade tare Alhaji Umar Pariya.

Wata sanarwa da Kakakin Shugaban Kasa Femi Adeshina ya fitar, Shugaba Buhari ya ce rasuwar Alhaji Pariya ta girgiza shi.

Sannan ya yi masa addu’ar Allah Ya yafe masa kura-kuransa tare da bai wa Atiku da iyalansa hakurin rashinsa.

Shugaba Buhari ya ce, “Na samu labarin rasuwar hadiminka, Alhaji Pariya. Akwai kaduwa ganin yadda kuka dade tare da shi a matsayin mai taimaka maka. Ina addu’ar Allah Ya jikansa Ya kuma bayar da hakurin rashinsa.’’

Tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ne ya fara sanar da rasuwar Alhaji Umar Pariya a shafinsa na Tiwita a ranar Talatar da gabata, inda ya bayyana cewa an yi rashi babba.

Alhaji Umar Pariya babban na kusa da Atiku ne, kuma sun dade tare inda har Atiku ke cewa ya wuce hadimi a wurinsa, ya zama dan uwa.

Daga cikin wadanda suka aike da sakon ta’aziyarsa akwai, Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa Asiwaju Bola Tinubu da Barista Yakubu Dogara da sauransu.