Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Burina in buga wa Najeriya da Real Madrid  kwallo – Mujahid I. Sharif

Mujahid Ibrahim Sharif matashin dan wasan kwallon kafa ne da fitilarsa ke haskawa a Kungiyar Kwallon Kafa ta Jigawa Golden Stars wadda ta samu nasarar haurawa gasar  Firimiya daga ajin kwararru a karshen kakar wasa ta bana. A hirarsa da Aminiya,ya bayyana yadda yake cike da burin ganin ya taka wani matsayi a fagen tamola:

 

ADVERTISEMENT

Mene ne takaitaccen tarihinka? Sunana Mujahid Ibrahim Sharif. An haife ni a Unguwar Kwana Hudu da ke yankin Birged a Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano, na yi karatun firamare a Firamaren Kaura-Goje sai na wuce makarantar sakandare ta Abbas Maje. Daga nan sai na fara harkar kwallon kafa.

ADVERTISEMENT

A ina aka fara koyon kwallo a layi ko a makarantar koyon kwallo?

Na fara koyon kwallon ne a layi kamar yadda mafi yawan ’yan wasa ke yi, sai dai daga baya na shiga wata makarantar koyon kwallo amma ita ma dai kamar ta layi ce. Sunanta, Ado Bora Sports Academy wato ABSA da ke a Kaura-Goje a nan Birged. Amma ba wata Academy ba ce wacce take da kudi ko samun tallafi na wasu manyan ’yan wasa, mu ne dai ’yan wasan muke yi wa kanmu komai da komai a wajen. Sai kuma shi Ado Bora da yake horar da mu bisa radin kansa saboda sha’awarsa da wasan da kuma kokarinsa na ganin cewa matasan ’yan wasan kwallo da suke a wannan yanki namu na Birged sun ci gaba sun kai manayan matakai a harkar kwallon kafa.

 

Wadanne kungiyoyi ka buga wa kwallo kawo yanzu?

Na fara buga wasa ne a wata kungiya mai suna Zage United wacce take a Rukuni na Biyu a jiha daga nan sai na koma kungiyar kwallon kafa ta Shinge wacce a lokacin tana a matakin Tofa ne. Daga nan na wuce wata kungiya mai suna Inted wacce take a ajin ’Yan Dagaji (Amateur), inda daga nan kuma na wuce fitacciyar kungiyar nan da take Birged mai suna Cosmos United.  A farkon bana kuma daga Cosmos sai na koma inda nake a yanzu wato Kungiya Jigawa Golden Stars inda a halin yanzu muka kai tsallaka zuwa Rukunin Firimiya da ita.

 

A ina ka fi kwarewa a cikin fili?

Ni dan wasan gaba ne amma ta gefe.

 

Wadanne nasarori ka samu kawo yanzu?

Alhamdulillah, in ka lura za ka ga tunda na fara kwallo daga matakin unguwa a kullum kara gaba nake yi. Da farko ina mataki na jiha na wuce zuwa na ajin marasa kwarewa ga shi kuma yanzu cikin taimakon Allah na kai ajin kwararru wadanda suka dauki kwallo a matsayin sana’a (professional). Kuma na kasance wanda ya fi cin kwallaye a gasar don haka ina godiya ga Allah da Ya ba ni wadannan nasarori a cikin kankanen lokaci.

 

Kwallaye nawa ka ci wa kungiyarka ta Jigawa?

Alhamdulillah a cikin wasannin sada zumunta guda 10 da na buga wa Jigawa na samu nasarar zura kwallaye 8. A wasanni 3 kuma na Kofin Kalubale na Jiha da na buga na ci kwallaye 3. Sannan a wasan da muka buga na Kofin Kalubale na Kasa da Kungiyar Bendel Insurance nan ma na samu nasarar zura musu kwallo a raga. Sai kuma a wasannin da muka kammala wadanda suka ba mu nasarar kaiwa gasar Firimiya na buga wasanni 8 kuma na ci kwallaye 7 wanda haka ya sanya na kasance wanda ya fi kowa zura kwallo a wannan mataki.

 

Yaya kake ji a yanzu da kuka tsallako zuwa gasar Firimiya?

A gaskiya ba zan iya misalta farin cikina ba. Kuma ina fata wannan ya zamanto mana alheri a nan gaba a cikin wannan sana’a ta kwallon kafa da muka fara kuma muke sa ran in Allah Ya ba mu nasibi a ciki za mu kai kololuwa da yardarSa.

 

Mene ne burinka a nan gaba a wannan sana’a ta kwallon kafa?

A gaskiya tunda yake na yi sa’ar fara wannan sana’a da karancin shekaru, ina sa ran a nan gaba cikin yardar Allah zan wakilci kasata Najeriya a matakai daban-daban kuma ina fatar zuwa kasashen Turai in buga wa manyan kungiyoyi irin su Real Madrid kwallo.

 

Wane dan wasa ne kake koyi da shi?

Dan wasan da nake kwaikwayo kuma nake koyi da shi saboda irin aikinsa nake yi a cikin fili shi ne Cristiano Ronaldo.

 

Ko kana ganin kafa makarantun koyon kwallo da ake kira academy na taimaka wa ’yan kwallo masu tasowa?

A gaskiya idan ka yi la’akari da yadda muke tasowa muna shan wahala don babu wanda yake tallafa wa matasa masu son yin wannan harka ta kwallo. Akwai matasa masu dimbin basira musamman a Arewacin kasar nan, amma saboda babu wani jigo da zai tsaya musu ko ya ba su shawara a karshe sai ka ga mutum ya gama kwallonsa a layi. Don haka idan za a samu irin wadannan makarantu a nan za su taimaka sosai.

 

Wace shawara za ka ba matasan ’yan kwallo kamarka?

Shawarata ga matasan ’yan kwallo ita ce su je makaranta kuma su jajirce ga koyon wasan tare da kasancewa masu juriya da nuna da’a a duk inda suka samu kawunansu.

 

Wane kalubale kake fuskanta a cikin wannan harkar ta kwallon kafa?

A gaskiya a halin yanzu dai babu wasu kalubale da yawa, dama dai nakan fuskanci kalubale ne wajen samun kayan wasa irin su takalma wadanda wani lokaci sai ’yan uwa da abokan arziki sun saya mini, amma yanzu cikin ikon Allah ina ga wannan ya kau.

 

Wane dan wasa ne ka fi jin dadin taka leda tare da shi?

Dan wasan da na fi son taka leda tare da shi shi Abdullahi Musa Lalan sai kuma wani yayana Ali Musa Kalla.

 

Wace kungiyar wasan kwallo ke burge ka a cikin kungiyoyin rukunin manya a Najeriya?

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars. Domin irin yadda suke kara wa Arewa martaba a fannin wasa ta hanyar yin fice da lashe gasanni da dama.

 

Wane kira za ka yi ga gwamnatn Jihar Jigawa don ba ku kwarin gwiwa ku ci gaba da samun nasarori a wasannin da za ku shiga na Firimiya?

Suna bakin kokarinsu amma duk da haka ina kira musamman ga Gwamnan Jihar Jigawa ya ci gaba da tallafa wa wannan kungiya domin mu samu damar ba da tamu gudunmawa wajen daga darajar Jigawa Golden Stars da Jihar Jigawa da yankinmu na Arewa da kasa baki daya.  A karshe ina godiya ta musamman ga masu horar da mu musamman babban Kocinmu Rabi’u Tata.