✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in dora daga inda mahaifina ya tsaya wajen taimakon al’umma -Hafsat Ado Damaturu

Hajiya Hafsat Alhaji Ado Damaturu ’yar gogaggen dan siyasar nan na Jihar Yobe ne, marigayi Alhaji Ado Damaturu, wanda shi ne zababben Shugaban Karamar Hukumar…

Hajiya Hafsat Alhaji Ado Damaturu ’yar gogaggen dan siyasar nan na Jihar Yobe ne, marigayi Alhaji Ado Damaturu, wanda shi ne zababben Shugaban Karamar Hukumar Damaturu na farko lokacin da tana karkashin Jihar Borno kafin kirkiro jihar. Ya yi zamani da Mohammad Goni da Waziri Ibrahim mahaifin Minista Khadija Bukar Abba. Ita ma ta bi sahun mahaifinta domin yanzu haka ita ce Kansilar Damaturu ta Tsakiya kuma Shugabar Kungiyar Kansilolin Jihar Yobe (Councilors Forum). Kuma  ita ce Kakakin Kungiyar ta Najeriya.

A zantawarta da Aminiya

 ta bayyana tarihinta  da

nasarorin da ta samu

a rayuwa:

Rabilu Abubakar, a Damaturu

Tarihina:

Sunana Hafsat Alhaji Ado, ni ’yar asalin garin Damaturu ce, an haife ni a Unguwar Hausari da ke Damaturu a Karamar Hukumar Damaturu a Jihar Yobe. An haife ni ranar 1 ga Fabrairun 1970. Mahaifina marigayi Alhaji Ado Damaturu dan siyasa ne wanda aka zabe shi ya Shugaban Karamar Hukumar Damaturu, ya kuma rike shugabancin Jam’iyyar GNPP a lokacin mulkin Alhaji Aliyu Shehu Shagari. Alhamdulillah bayan na kai munzalin shiga makaranta sai iyayena suka saka ni a firamare ta Njiwaji da ke Damaturu da na kammala sai na samu tafiya GSS da ke Damaturu inda na kammala karatun sakandare, sai aka yi min aure sannan na samu aiki a Hukumar Yaki da Jahilci (Agency for Mass Education) da ke nan Damaturu, inda aka dauke ni a matsayin Home Instructor a sashen ilimin tattali da kula da gida (Home Economics), da ma na iya dinki saboda mahaifiyata tela ce kuma a wajenta na koya, da sana’ar na tashi. Daga nan sai na tafi  kwas a Agency for Mass Literacy a Maiduguri inda na yi kwas kan Tattalin Gida, na yi satifiket na shekara daya a 1996, bayan nan sai na sake komawa Kwalejin Koyon Harkokin Mulki da Kasuwanci (College of Administratibe and Business Study- CABS) da ke garin Potiskum a nan Jihar Yobe inda na karanta bangaren Ci gaban Al’umma (Community Debelopment and Mass Education) daga  shekarar 2005 zuwa 2007. A shekarar 2011 kuma sai na shiga harkar siyasa gadan-gadan, da aka zo yakin neman zabe sai aka ba ni Shugabancin Mata a mazabata, a shekarar 2013 sai aka ba ni Mai ba da Shawara a Karamar Hukuma har zuwa 2015, daga nan sai na tsaya takarar kansila a mazabata a Damaturu ta Tsakiya a shekarar 2017, sai Allah Ya ba ni nasara na ci zabe inda na kasance mace guda daya a cikin maza sannan kuma ni ce Shugabar Kungiyar Kansiloli ta Jihar Yobe (Yobe Councillors’ Forum).

 

Nasara:

Nasarorin da na samu suna da dama domin na taimaka wa jama’ar mazabata wajen yi musu wakilci nagari, bayan nan aikin da na yi wanda ya burge ni kasancewata wakiliya ta al’ummar mazabata shi ne akwai wata yarinya  mai shekara 15 da ta gamu da ciwon sankaran mama kuma iyayenta masu karamin karfi ne, sai na yi tsayin daka sai da aka yi mata aiki aka yanke shi, aikin ma sau biyu aka yi mata da aka yanke mata maman sai aka sake yi mata wani aiki inda aka yanki naman cinyarta aka lika a wurin ta kuma samu lafiya ta ci gaba da karatunta.

 

Kalubale:

Kalubalen da nake samu ba mu da mata da suke shiga harkokin siyasa, ni kadai ce mace zababbiya a cikin maza, hakan ya sa nake ganin akwai kalubale da dole sai na tashi tsaye wajen kira ga mata don su rika fitowa ana damawa da su a siyasa..

 

Burina a rayuwa:

Burina shi ne na zama cikakkiyar ’yar siyasa kuma gogaggiya kamar mahaifina

Alhaji Ado Damaturu don na gaje shi duk da ma dai na fara kama hanya, don in rika taimaka wa jama’a kamar yadda na tashi na ga mahaifin nawa yana yi saboda in dora daga inda ya tsaya.

 

Tufafi:

Tufafin da na fi son sakawa su ne doguwar riga in yafa gyale saboda duk wanda ya gan ni ya san cewa kamila ce kuma ’yar Arewa cikakkiya saboda tufafi shaida ne da ke tabbatar wa mutane yadda za su dauke ka da zarar sun gan ka.

 

Hutu:

A lokacin da na samu hutu, ina hutuna ne a Najeriya tare da ziyarar ’yan uwana a kauye. Ba na zuwa wata kasa ko wani gari daban don yin hutu domin tafiya hutu wani gari ba zai ba ka dama ka ziyarci ’yan uwa ba ballantana ka san matsalolinsu har ka taimaka musu.

Kungiyoyi:

Ina cikin kungiyoyi da dama. Yanzu haka ni ce Amirah ta Kungiyar Mata Musulmi  (FOMWAN) reshen Karamar Hukumar Damaturu tun daga shekarar 2016 zuwa yanzu, sannan ni ce Mataimakiyar Shugaba ta II ta Majalisar Mata ta Kasa (NCWS) reshen Jihar Yobe sannan ni mamba ce a kungiyar Mata Musulmi ta Muslim Sister’s Organization (MSO) reshen Jihar Yobe.

 

Kasashen da na je:

Kasar Saudiyya kadai na taba zuwa kuma na je har sau tara. Ban da nan babu kasar da na je kuma.

 

Yawan iyali:

Alhamdulillah! Ina da ’ya’ya 5 maza 3 mata 2 kuma dukkansu ina kula da tarbiyyarsu.

 

Shawara ga Iyaye:

A matsayina ta mace ina bai wa iyaye shawarar cewa su sanya ’ya’yansu a makaranta su yi ilimin zamani ba ya ga na addini da suke yi domin ilimi shi ne hasken rayuwa. Idan mace ta zama ba ta da ilimi rayuwa za ta zame mata baibai domin ko a gidan miji ba za ta iya kula da harkokin gidanta ba ballantana tarbiyar ’ya’yanta. Sannan ina jan kunnen iyaye da kada su bar ’ya’yansu mata suna gararambar talla ko a ce za a yi musu auren wuri ba tare da sun yi karatu koda sakandare ba. Za ka ga wadansu iyayen maimakon su sa ’ya’yansu a makaranta sai a same su a wajen talla inda a nan ne ake fara lalata tarbiyarrsu. A karshe ina shawartar iyaye su san cewa bambanta tsakanin maza da ’ya’ya mata kuskure ne don ilimantar da ’ya mace ya fi namiji muhimnanci.