✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in ga mata sun ci gaba a fannin ilimi – Dokta Amamatu Yusuf

Dokta Amamatu Yusuf jajirtarta ce a Jihar Sakkwato kan ilmin ’ya’ya mata wacce mutane ke kallo abin koyi ga harkar ilmin mata, don rayuwarta da…

Dokta Amamatu Yusuf jajirtarta ce a Jihar Sakkwato kan ilmin ’ya’ya mata wacce mutane ke kallo abin koyi ga harkar ilmin mata, don rayuwarta da tunaninta da karfinta sun karkata ne kan yadda yara mata za su samu ilmi, abin da ake gani ya zama silar da ya sanya Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ba ta mukamin Mai Ba shi Shawara Kan Ilmin Mata don ta bayar da gudunmuwa ga ci gaban Jihar Sakkwato, Aminiya ta zanta da ita kan rayuwarta.

Tarihinta:

Sunana Amamatu Yusuf.   An haife ni a garin Tambuwal. Mahaifina Attahiru Gandi da mahaifiyata Amina Waziri sun aminta da sanya ni makarantar firamare ta cikin gari wacce mahaifina yake shugabanta a lokacin. Duk  sa’o’ina da na kasa da ni makarantar suka yi. Da na kare ne sai na wuce Sakandare ta mata a Kano (GGC Dala), na yi aji daya a can.   Saboda rashin lafiyar da ke damuna mahaifina ya mayar da ni gida Sakkwato na cigaba da karatu a Sakandaren  ’yam  mata ta jiha (GGC a yanzu). Da na kare aka yi mini aure.. Bayan nan,  sai aka ce ana bukatar wadanda za a sanya jami’ar tarayya da ke nan (Sakkwato) wacce za a bude a shekarar 1976 na nemi gurbin karatu na share fagen shiga Jami’ar kuma na samu amma da na kammala sai na shiga Kwalejin Horar da Malamai ta jiha (COE) don sha’awar da nake da ita kan karantarwa. Bayan na kare bautar kasa ne na bi mijina zuwa Amurka da muka je can ne na yi karatun digirina na farko a Jihar  Uhayo.   Bayan nan muka dawo gida lokacin samun aiki ba ya da wahala kuma mun yi karatun a tallafin karatu na jiha sai na ci gaba da aikin da na fara na karantarwa (STC). Da maigidana ya samu aikin gwamnatin tarayya a Legas sai muka koma can, sai na nemi gurbin karatu na yi digirina na biyu (Masters) a ilmin sanin halayyar dan Adam (Education sychology), da na kare na samu aiki da Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (National Unibersity Commission) a lokacin ofis dinsu yana Legas. Da suka dawo Abuja ne suka ba ni damar tafiya karo karatun digirina na uku (Phd) a Jami’ar Abuja, na karba da hannu biyu na tafi na yi karin karatun. Hukumar Inshorar Lafiya ta kasa (NHIS) da aka bude ta ne na koma can da aiki ina tare da su har lokacin da Allah Ya yi wa maigadana rasuwa a shekarar 2013 na ga ba zan iya aikin ba, na ajiye duk da lokacin ritayata bai yi ba don ina da sha’awar dawowa gida in taimaka wa Jihata Sakkwato. Allah cikin ikonSa ya kaddare ni da samun wannan aikin da nake yi na bai wa Gwamna Sakkwato Shawara kan illmin ’ya’ya mata.

 kalubalen da na fuskanta:

kalubale bai fi na rayuwa ba.  Ina yi wa Allah godiya nasarorin da na samu sun fi yawa kan kalubale. Allah Ya halicce ni cikin Musulunci ya hada ni da uwayen da suka yi mini tarbiyya da koyar da ni addini kan hanyar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW), an yi min iaure cikin lokaci ina tare da maigidana har mutuwa ta raba mu. Halin da na shiga bai wuce na  rasa masoyinka  ko wani abu da ka mallaka kuma ba za a ce masa kalubale ba don kowa zai yi murna sannan ya yi kuka, wannan duk halin rayuwa ne. Na yi karatuna ban samu cikas ba, aure bai hana ni karatu ba.

Burinta na kuruciya:

A lokacin da nake yarinya gidanmu na tashi na samu karatu shi ne gaba da komai, sai wannan ya shiga raina ban da buri kamar na yi ta karatu, ko wasan yarinta da muke yi ta dalibai, da malami muke yi don karatu ne kawai muka sanya a gaba.

 Burinki na rayuwa ya cika:

Sai godiyar Allah. Na yi aiki, na ajiye aikina da hannuna ba tare da na samu wata matsala ba. Kuma Allah Ya taimake ni na kara samun wannan da nake yi na Mai bai wa gwamna shawara.   Gwargwado burina ya cika, na samu abubuwan da duk nake bukata, nagode Allah.

 Abin da take son a tuna ta da shi:

Kowane mutum yana son a tuna da shi a  ayyukkan alheri da ya aiwatar. Ina farin cikin na gama da iyayena lafiya kuma ba ni da wani hali da mutane ke yin tir da shi. Ina da iyali da muke rayuwar musulunci tare da su. Ina son mutane su tuna da ni, ni mai tausayi ce ga mutane da son cigaban ilmin mata. Ban da wanda nake kyashi ko son ya samu matsala. Na kan bai wa wacce nake tare da ita shawara gaskiya da alheri ko da ita ba ta so hakan ba. Na kan yi kokarin sanya basirata inda za ta amfani jama’a.

Iyali:

Allah Ya azurta ni da yara biyar, hudu maza, mace daya. Ya ba ni ’yan uwa masu yawa a gefen uwa da uba da masoya wadanda tun muna yara muke tare cikin aminci da gaskiya.

Yawan mata a Makarantu:

Sai godiyar Allah.  kididdiga  ta nuna mata masu zuwa makaranta sun karu a Jihar Sakkwato.   In ka tafi makarantun mata na jiha za ka zaci ba wata yarinya da ke zaune a gida,  akwai cigaba don iyaye sun fahimci karatun mata na da amfani, sabanin in da aka fito.   Mata suna yin talla amma mafi yawansu suna yi ne bayan an tashi makaranta. Gwamnatin Sakkwato na iyakar kokarinta wajen tallafawa ’ya’ya mata ga karatunsu. Ana bayar da tallafin karatu na kudi ga ’ya’ya mata don saya masu tufafin makaranta, takalmi, jaka da sauransu.   Gwamnati ta ragewa iyaye nauyi ne don su samu sukunin kai yaran makaranta.

Tarbiyyar mata matasa a yau:

Gaskiya mun san an samu ragi a tarbiyyar maza da mata, saboda abubuwan da suka shigo wadanda can baya ba mu da su.  Sun taka rawar tabarbarewar tarbiyya musamman mata. Sakkwato na da tarihi na addinin Musulunci, wannan kwarai ya taimaka wajen samun karancin mata masu shaye-shaye, suna zuwa makaranta da suturar da addini ya aminta da ita.

Burin ki na rayuwa a gaba:

Ba wanda ba shi da burin da yake son ya cika a gaba cikin rayuwarsa, abin da nake so bai fi na taimaki jiha ta Sakkwato ba, na kara farfado da ilmin mata, su cika makarantun gaba ga sakandare, in sun samu ilmi ne kadai za su iya amfanar da kansu, kuma duk abin da mace ke son zama za ta iya.

Macen da ta fi burgeki:

Ina da ita sosai na tashi a gidanmu ina da wata anti ita ce babba a gidan gaba daya ta zame mana kamar uwa, tana dora mu kan hanyar da za mu taimaki kanmu, madogara ce a wurinmu, Allah Ya jikanta da rahama.

kasashen da ta ziyarta:

Na ziyarci k kamar Amurkaa Amerika da na dade a can.   Na je Ingila, Afika ta Kudu, Zimbabuwe, Zambiya, Oman, Uganda, Dubai, Angola da Ruwanda da sauransu.

Kira ga mata:

Mata su fito a yi gwagwarmaya da su a harkar siyasa da aikin gwamnati da sauran mu’amala na rayuwa. Su kara karatu.   Akidar rashin son karatu su ajiye lokacinta ya wuce.   Maza ma sun fi son su auri mai karatu. Mai ilimi ce kawai ke taimakon gidan mijinta da gidansu.   Mata ina kira gare ku da ku yi karatu mai amfani.