Search
Subscribe
Burinmu hada kan ’ya’yan jam’iyyarmu  ta APC – Bashir Yusuf

Burinmu hada kan ’ya’yan jam’iyyarmu  ta APC – Bashir Yusuf

Alhaji Bashir Muhammad Yusuf, shi ne Shugaban Kungiyar ’Yan Takara a Jam’iyyar APC na Kasa, wadda ta kunshi wadanda suka yi takara a zaben fid-da-gwani ba su samu nasara ba. A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana dalilan da suka kafa kungiyar:

 

Mene ne makasudin kafa wannan kungiyar?

Bayan mun tsaya takara a zaben fid-da-gwani ba mu samu nasara ba sai muka ga ya kamata mu hada kanmu, kada mu yi fushi mu ce jam’iyya ba ta yi mana daidai ba, shi ne muka kafa wannan kungiya. Domin mu ba da gudunmawarmu don samun nasarar jam’iyyarmu ta APC. Mun ga ya dace mu zama tsintsiya madaurinki daya kuma mu yi magana da murya daya, don tabbatar da Jam’iyyar APC ta kai gaci, kuma Allah cikin ikonSa hakarmu ta cimma ruwa. Kuma a matsayinmu na ’ya’yan Jam’iyyar APC idan wani abu ya faru mukan tashi tsaye mu tabbatar da ganin a yi abin da ya kamata a matakin jiha ne ko tarayya don ci gaban al’ummarmu.

Shin wannan kungiya tana da rajista ce ganin kungiya ce ta jam’iyyar siyasa?

Kungiyar nan duk da ta siyasa ce tana da rajista tun a shekarar 2014, kuma ba kungiya ce da ta kunshi ’yan takara na siyasa kawai ba, ta kunshi wadanda suka tsaya takara ba su samu nasara ba da wadanda suka ci zabe. Su ma sun kasance ’ya’yan wannan kungiya duk da a dalilin cin zaben sun bar kungiyar, to amma dole su ba da gudunmawarsu don ci gaban wannan jam’iyya ta APC don ita ce sanadiyar zuwansu wannan kujera.

Bayan kafa wannan kungiya a 2014, an yi zaben 2015,  akwai wani sakamako da ’ya’yan kungiyar suka samu, kan gudunmawar da suka bayar game da samun nasarar Jam’iyyar APC?

Alhamdulillah da yawa wasu sun amfana daga gwamnatin Shugaban Muhammadu Buhari a 2015 zuwa 2019. A ce ba a mfana ba ya zama butulci da rashin godiya ga Ubangiji. Kuma a 2019 wadansu da yawa daga cikinmu an yi takarar saboda muna da mambobi kamar 9000 a kasar nan, kuma gudumawar da muka bayar a zaben nan ina ganin idan ba mu ba da kashi 99 to mun ba da kashi 90 ganin yawan mambobinmsu. Domin duk wanda ya fito takara yana da magoya baya da babu wanda ya san adadinsu, don haka nake ganin mun taka muhimmiyar rawa a zaben da ya gabata. An yi zabe an gama har an nada ministoci fatarmu wannan gwamnati ta Baba Buhari ta sake duban ’ya’yan wannan kungiya da suka ba da muhimmiyar gudunmawa wajen samun nasararsa a saka musu da ba su mukamai don su kula da wadanda suke bayansu a mazabansu.

Wadansu kan yi fushi su kaurace wa jam’iyyarsu su koma wata, shin kun samu wannan matsala a zaben 2019?

Gaskiya ba mu samu ba, saboda kanmu a hade yake kuma muna yin abin ne domin kishin  Jam’iyyar APC. Kuma ba mu da shakku a kan jam’iyyarmu. Kungiya ce da muka kafa ta mutanen da suka san ciwon kansu wadanda jama’arsu ne a gabansu ba son zuciyarsu na. Kuma duk wanda ya tsaya takara mutum ne kamilalle wanda ba ya da wani dauda da zai iya hana shi tsayawa kamar yadda doka ta tanada. Haka za ka tarar ba ya da matsala da al’ummarsa, don haka ya fito don ya jagorance su ko ya wakilce su.

Kamar yadda ka fada ’yan takarar sun ba da gudunmawa, sai dai akwai korafe-korafe da shari’u a kotuna. Shin a kungiyarku wacce gudunmawa kuke ba wadannan ’yan takara don su samu nasara?

To tsarin Mulkin Kasa ya bada dama ko a siyasance ko ba a siyasa ba, idan aka yi maka abin da bai dace ba, ka kai kara kotu. Saboda haka ba mu da wani dalili da za mu hana wani mambanmu zuwa kotu idan ya san ba a kyauta masa ba. Abu na biyu kotu ita ce kawai za ta iya tantance cewa abin da aka yi daidai ne ko ba daidai ba. Kungiya ba ta da wannan hurumi, abin da kawai za ta ba ka goyon baya shi ne idan ta tabbatar ba a yi maka adalci ba, za ta bi hanyar da ta dace na dimokuradiyya ta sake kai kara kotu wanda idan abin da muke da shi ya tabbata gaskiya ce, za mu yi duk abin da ya kamata don karbo maka hakkinka.

Ka fito neman takarar dan Majalisar Wakilai daga Mazabar Dala, sai ga shi tun a zaben fid-da- gwani ba ka samu nasara ba, yaya alakarku take a jam’iyyance da  gwamnatin Jihar Kano?

Gwamnatin Jihar Kano muna da kyakyawar alaka da ita, domin Jihar Kano jihata ce. Kuma idan ka dubi irin ayyukan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yake aiwatarwa a Kano ai duk dan Kano ba ya da abin fadi sai dai ya ce sam barka da samun Gwamna irin ganduje. Kuma fitowata takara da rashin samun nasarata a zaben fid-da-gwani wannan lamari ne daga Allah, don haka babu wani abu da zai taba alakata da jam’iyyata ta APC ko Gwamnatin Jihar Kano. Ina yin biyayya ga jam’iyya da girmama Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayinsa na uba kuma jagoran APC a Kano. Kuma a shirye nake in ba da duk wata gudunmawa ga ci gaban jihar da kasa baki daya.

Wadansu na korafin cewa Shugaban Kasa ya dauki tsofaffi daga Jihar Kano kuma ba ’yan siyasa ba ya nada su ministoci. Yaya kake ganin wadannan maganganu?

Mu ’ya’yan Jihar Kano, sai mu gode wa Allah sannan mu gode wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya ba mu ministoci biyu. Kuma zance wai ba ’yan siyasa ba ne, shin me ake bukata? Su yi wa al’umma aiki, kuma duk wadanda aka dauko kwararraru ne, Janar Bashir Magashi da aka ba Ministan Tsaro, tsohon soja ne, za a ce bai san harkar tsaro ba ne? Kowa ya ga rawar da ya taka a aikin soja. Don haka ina ganin zai ba da gagarumar gudunmawa wajen dakile kalubalen tsaro da ke damun kasar nan. Shi kuma Ministan Gona dan Arewa ne, kuma a Arewa ne aka fi noma. Akwai wanda zai ce Sabo Nanono bai san harkar noma ba n? Don haka wannan zance da wadansu ke yi bai ma dace ba. Fatarmu ga ministocin namu, ita ce su tuna amana ce aka ba su, su tsaya su taimaka wa wannan gwamnati ta samu cimma nasara a dukkan ayyukan da ta sa a gaba, ta kuma cika alkawuran da ta yi wa al’umma lokacin yakin neman zabe.

Mu kuma jama’ar kasa musamman ’yan siyasa mu rika yin komai bisa tsari, kada adawa ta sa kana ganin gaskiya ka guje mata. Wannan gwamnati ta fara aiwatar da abubuwan kyautata rayuwar al’ummar kasar nan, saura kawai mu ci gaba da yi mata addu’a.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin