✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Carlo Ancelloti ya zama kocin Real Madrid

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayyana Carlo Ancelotti, tsohon kocin kulob din PSG da ke…

A ranar Talatar da ta wuce ne kulob din Real Madrid da ke Sifen ya bayyana Carlo Ancelotti, tsohon kocin kulob din PSG da ke Faransa a matsayin sabon kocinsa.
A shekaranjiya Laraba ne kuma kulob din ya yi bikin kaddamar da kocin ga bainar jama’a a harbar filinsa da ake wa lakabi da Santiago Bernabeu.
Ancelotti wanda ya samu nasarar lashe kofin zakarun kulob-kulob har sau biyu (UEFA Champions League) a shekarar 2003 da 2007 a lokacin da yake horarwa a kulob din AC Milan da ke Italiya ya samu nasarori da dama a kulob daban-daban.
Ya taba lashe kofunan European Cup sau biyu baya ga lashe gasar rukuni-rukuni da ya yi a Italiya da Ingila da kuma a Faransa.
Don haka za a iya cewa babu irin kofin da ake ji da shi wanda kocin bai lashe ba.
Wata sanarwa da kulob din Real Madrid ta fitar a kafar sadarwar ta ce “Muna sanar da duniya cewa mun kulla yarjejeniya da sabon kocinmu Carlo Michelangelo Ancelotti da zai fara aiki da mu a kakar wasa ta bana”.
An ce kocin ya kulla yarjejeniyar shekara uku ne a tsakaninsa da kulob din na Madrid da kuma albashi mai tsoka.
Tun bayan da tsohon kocin kulob din Jose Mourinho ya canza sheka zuwa kulob din Chelsea da ke Ingila sai yanzu kulob din ya maye gurbinsa.
Shi kuma Carlo Ancelotti, tsohon kulob dinsa na PSG ya maye gurbinsa ne da tsohon mai horar da kasar Faransa Laurent Blanc.
Tun lokacin da aka fitar da Faransa a gasar cin kofin Nahiyar Turai (Euro 2012) a matakin kusa da na karshe watau kwata-fainal kocin yake zaman jiran tsammani sai a yanzu da ya koma kulob din PSG da ke Faransa don cigaba da aikin horarwa.