✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Charly Boy ya jagoranci zanga-zangar dawo da Diezani gida

Mista Charles Puta wanda aka fi sani da Charly Boy ya jagoranci tawagar Kungiyar Wawacinmu Ya Isa wacce ake kira da Turanci “Our Mumu Don…

Mista Charles Puta wanda aka fi sani da Charly Boy ya jagoranci tawagar Kungiyar Wawacinmu Ya Isa wacce ake kira da Turanci “Our Mumu Don Do” zuwa hedikwatar Hukumar EFCC da ke Abuja inda suka nemi Hukumar ta dawo da Tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur, Diezani Allison-Madueke daga Kasar Birtaniya don ta fuskanci shari’a kan zargin cin hanci da ake yi mata.

Charly Boy wanda ya yi magana a madadin kungiyar ya bukaci Hukumar EFCC ta dauki matakan gaggawa don tabbatar ta dawo da Tsohuwar Ministan gida.
“Sakamakon zarge-zargen da ake yi mata na cin hanci da satar kudin gwamnati da ke yi wa Tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur, Misis Diezani Allison-Madueke, muna kira ga Hukumar EFCC ta dawo da ita don ta fuskanci shari’a”. Inji shi.
Ya ci gaba da cewa “Ya zama wajibi ta dawo gida ta wanke kanta idan kuma hakan ba zai yiwu ba ya zama wajibi a taimaka wa Birtaniya ta gurfanar da ita a gaban kuliya saboda batun cin hanci bai kamata a bari ya tafi haka ba”.