Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Cin fuska ce a taka mana tuta – Isra’ila

Firayi Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Isra’ila Tzipi Hotobely ya nuna rashin jin dadinsa bayan an gano wani hoto na Minista a Ma’aikatar Tsaron Jordan yana taka tutar kasarsu.

Hoton ya nuna Ministan na Jordan Mista Jumana Gheimat yana taka tutar Isra’ila lokacin da yake shiga wani taro.

ADVERTISEMENT

Tutar, an makala ta ce a kofar shiga dakin taron domin nuna rashin jin dadin yadda Isra’ila ta mamaye kasar Falasdinu.

Yadda ya taka tutar ta sa Isra’ila ta nuna rashin jin dadinta tare da neman bayani a kan dalilin yin haka.

ADVERTISEMENT

“Ma’aikatar Harkokin Wajen Isra’ila na kallon taka mata tutar kasarta da Ministan Jordan ya yi a matsayin cin fuska,” inji shi.

Daga baya Ma’aikatar Harkokin Wajen Jordan ta fitar da sanarwa inda ta tabbatar da cewa lalai tana girmama kowace kasa kuma tana son zama lafiya da girmama juna.

Haka kuma kasar Jordan ta kara da cewa Ministan ya shiga ginin ne ta asalin kofar shiga, sannan ginin da aka dauki hoton ba na gwamnati ba ne.

Kasar Jordan da Masar ne kadai suke da alakar diflomasiyya da kasar Isra’ila a cikin kasashen Larabawa a yanzu.