✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cin hanci da rashawa a Najeriya

Cin hanci da rashawa cuta ce da ke yaduwa a tsakanin al’umma, tana ci kamar wutar daji. Wannan lamari ba wai ga Musulmi ko Kirista…

Cin hanci da rashawa cuta ce da ke yaduwa a tsakanin al’umma, tana ci kamar wutar daji. Wannan lamari ba wai ga Musulmi ko Kirista ko ma wanda ba shi da addini. A kalla kowanne mutum ya shiga ciki, domin ta taba kowane bangare na al’umma.
Misali, ba a daukar mutum aiki sai ya bada cin hanci, yayin da wanda aka ba aiki shi kuma yakan hada kai da wanda ya daukeshi aiki, domin su sace kayan al’umma.
Ba shakka ba wai ma’aikaci ba ne kadai ke cin hanci. Hatta ‘yansanda da jami’an kwastam, sun karba ta sigar aikinsu, inda akan same su da cin hanci da rashawa fiye da sauran sassan al’umma. Misali jami’i mai bada hannu a tituna kan karbi cin hanci ga direba mai tukin ganganci, mai sudaddun tayoyi kuma maras lasisi.
Haka nan kuma, jami’in hana fasa kwari kan karbi cin hanci daga hannun dan simoga, ya kuma kyale shi ya tafi abinsa.
Haka dai, wannan sha’ani na cin hanci da rashawa ba ga ‘yansanda da jami’an kwastam kawai ya tsaya ba, abin ya nashe duk sauran sassa.
Ga misali:- jami’ai masu binciken kudi, kan karbi cin hanci ga jami’ai masu lura da bitalmali, su hada kai su ci amanar dukiyar al’umma. Haka nan jami’ai masu tattara haraji na kuma tara kudin shiga a kasa, kan hada kai da manyan ‘yan kasuwa su zabtare musu haraji. Abin ba a nan ya tsaya ba, manyan injiniyoyi masu kula da gine-ginen gwamnati kan karkatar da kayayyakin ginin gwamnati, don kaiwa wuraren da suke gini na kashin kansu.
Haka nan, jami’ai masu bada aikin kwangila kan ba da aikin ne kurum ga wadanda za su ba su kudin kaso goma da aka fi sani da (ten per cent). Kai hatta malaman jami’a kan ba da maki mafi romo ga kyawawan mata da suke kauna, wannan shi ne aikin baban giwa.
Wani abin dariya a wannan kasar shi ne yadda wasu mutane ke ta babatu kan batun cin hanci da rashawa, amma a waje guda kuma su ne mutanen da za ka taras suna gina manyan gidaje ta haramtacciyar hanya. Kowane mutum sai kaji yana ta zance barkatai, yana wai cin hanci da rashawa ya yi yawa a wannan kasa, shin abin dubawa shi ne, mutum nawa suka tsira daga cin hanci ko karbar rashawa? Mutum nawa ne suke da gaskiya?
Da yawa daga cikinmu ba mu taba tsayawa mun yi tunani game da illar cin hanci da rashawa ba, ta yadda makudan kudin haraji ke zurarewa daga shiga aljihun gwamnatin tarayya da ta jihohi duk shekara ta fuskar ma’aikata da jami’an gwamnatin da ke karbar cin hanci da rashawa.
Tabbas cin hanci da rashawa kan zubar da mutunci da kuma kimar dan Adam ta yadda tunaninsa da duk wani aiki nasa kan zamo a wofi. Tunanin yin aiki tukuru ne ma yake zama tsohon ya yi ta yadda ake neman maye gurbinsa da lalaci. Abin da mutane suka fi sha’awa yanzu shi ne yin arziki cikin gaggawa, don a ganinsu gaskiya a yanzu ba ta biya.
Yayin da jama’a ta rufe idonta take neman tara dukiya ta kowane fanni, al’amura suka kazanta tabbas tagwayen bala’ai na cin hanci da rashawa kan samu gindin zama, gaskiya kuwa ta koma baya. Idan haka ta kasance al’umma kan zamo cikin duhu har abada.
Shin akwai wani kyakkyawan fata kuwa ga Najeria? Akwai wata hanya mafificiya kuwa? Wane likita ne zai mana maganin wannan tagwayen masifu na cin hanci da rashawa?
Lokacin da sojoji suka karbe mulkin kasar nan sun yi alkawarin murkushe cin hanci da rashawa amma yaya batun yake ne a yanzu? Cin hanci da rashawa yaci gaba dayin muni da kuma yaduwa ta yadda muninsa da girmansa ba zai iya misaltuwa ba.
Ba shakka, a tunani na akwai kyakkyawan fata na samun sabuwar Najeriya, muddin zamu hada kai muyi aiki tukuru, mu hana zuciyarmu abin da take so na daga soye-soyen ta sai mu murkushe cin hanci da rashawar  da ya yi katutu a zukata. A kalla dai dole mu yaki zuciyarmu mu dai-daita sahunta.
A nata bangaren, dole ne gwamnati ta yi aiki sosai akan dokokin horo da kuma sakamako akan duk mutumin da aka kama da laifin cin hanci da rashawa. A rika hukunta  duk wanda aka kama da laifin cin hanci da rashawa, ba tare da la’akari da matsayi ko mukaminsa ba.
Abin kaico sai a kama dan sane wanda abin da ya sata bai fi Naira guda ba, amma a turashi gidan yari, a waje guda kuwa a samu wani jami’in gwamnati ya yi awon gaba da sama da Naira dubu dari (N100,000) daga lalitar gwamnati, amma a barsa ya tafi abinsa.
Haka a daya bangaren yana da kyau bayan hukuma ta hori wanda aka kama da laifi ta kuma karrama wanda aka samu da gaskiya da amana akan aikinsa. Wanda zai tabbatar wa jama’a ita gaskiya sunanta gaskiya, domn kuwa ba a taba cewa gaskiyar mutum ta kare ba, sai dai ace karyarsa ta kare, Allah yasa mu dace.

 AUWALU AHMAD NAKARKATA DAMBATTA                                                                       
Jagoran wayar da kan matasa na Arewacin Najeriya
E-mail: [email protected]
08102661967, 08157382865