✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cin yankakkun kajin da ake shigowa da su daga waje na da illoli

Wani masani kan harkokin kiwon kaji a Najeriya, mai suna Mista Oduware Efe ya yi gargadin cewa, akwai illoli masu yawa game da cin yankakkun…

Wani masani kan harkokin kiwon kaji a Najeriya, mai suna Mista Oduware Efe ya yi gargadin cewa, akwai illoli masu yawa game da cin yankakkun kajin da ake shigowa da su daga kasashen waje. Mista Oduware Efe ya yi wannan gargadi ne, lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a birnin Legas.

Ya ce, akwai illoli da dama ga lafiyar jama’a  game da cin naman yankakkun kajin da ake shigowa da su daga kasashen waje, musamman irin sinadaran da ake sanya wa kajin, don kada su lalace kafin a shigo da su.

“Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) da sauran cibiyoyin bincike na jami’o’in kasar nan, sun tabbatar da cewa, a binciken da suka yi kan sinadaran da ake sanya wa irin wadannan kaji, don kada su lalace kafin a shigo da su suna da cutarwa ga lafiyar jama’a, domin irin wadannan sinadarai ne ake sanyawa a jikin gawarwakin mutane, domin kada su rube,” inji shi.

Ya ce, kuma shigowa da irin wadannan yankakkun kajin yana yi wa tattalin arzikin kasar nan zagon kasa. Domin suna kashe kasuwar kajin da ake kiwatawa a kasar nan. Don haka ya yi kira ga al’ummar Najeriya, su guji cin naman yankakkun kaji da ake shigowa da su daga kasashen waje.