✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Cittar da ake nomawa a Najeriya ta fi daraja a kasuwar duniya – Dauda Nuhu

Shugaban kungiyar Manoman Citta da Kasuwancinta a Ciki da Wajen Najeriya (MAGbAN) Mista Dauda B. Nuhu ya ce cittar da ake nomawa a Najeriya, ita…

Mista Dauda NuhuShugaban kungiyar Manoman Citta da Kasuwancinta a Ciki da Wajen Najeriya (MAGbAN) Mista Dauda B. Nuhu ya ce cittar da ake nomawa a Najeriya, ita ce tafi daraja kuma ta fi tsada a kasuwannin duniya. Mista Dauda Nuhu ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin taron da kungiyar ta shirya wa manoman citta don wayar musu da kai kan nomanta da kuma shirin da Gwamnatin Tarayya ta yi, na tallafa wa harkar noman citta a Najeriya a  garin Kwoi da ke karamar Hukumar Jaba a Jihar Kaduna.
Ya ce cittar da ake nomawa a Najeriya, masu hada magungunan zamani da na gargajiya a kasashen duniya suna amfani da ita: “Don haka Gwamnatin Tarayya take son ta hada manoman citta da masu saye da fitar da ita zuwa kasashen waje, ta tallafa musu don cittar ta kara samun daraja ta yadda kasar nan za ta rika samun kudaden shiga daga kasashen waje,” inji shi.
Shugaban ya ce sun yi zama da jami’an Ma’aikatar Gona ta Tarayya sau uku kan wannan kuduri na tallafa wa noman citta a Najeriya.
Mista Dauda Nuhu ya yi bayanin cewa sun kafa kungiyar ce ganin babu yadda za a yi a samu nasara kan kudurin da gwamnati take da shi na tallafa wa manoman citta sai  sun hada kai.
Ya ce sun zabi wannan yanki na Jaba ne don gudanar da wannan taro ganin cewa a duk Najeriya babu wurin da ake noman citta kamar yankin.
Ya yi kira ga manoman citta kan su hada kai su ba kungiyar goyon baya domin su ci gajiyar kudurin Gwamnatin Tarayya na tallafa musu.
A jawabin shugaban kungiyar wayar da kan matasa ta IYAMIDR Kwamared Okoduwa Solomon ya ce noma yana samar wa matasan kasar nan ayyukan yi da kashi biyu bisa uku. Ya ce idan aka rungumi noma a Najeriya, za a samar wa matasa ayyukan yi da za su dogara da kawunnansu.
Taron ya samu halartar manoman citta da sauran masu ruwa da tsaki kan harkar noman citta daga Kudu da Arewa sama da 200.
Tunda farko kafin fara gudanar da taron, tawagar shugabannin wannan kungiya sun kai ziyarar ban girma ga Sarkin Kwoi Dokta danladi Maude.