✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: A karon farko mutum sama da 200 sun kamu a Najeriya

A karo na farko ko an samu karuwar mutum sama da 200 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya. Alkaluman Hukumar Yaki…

A karo na farko ko an samu karuwar mutum sama da 200 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya.

Alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) sun nuna cewa a ranar Alhamis an samu mutum 204 da aka tabbatar sun kamu.

Da wannan sabon lissafin ne hukumar ta nuna cewa, “Zuwa karfe 11.50 na daren 30 ga watan Afrilu, mutum 1,932 ne aka tabbatar da sun kamu da COVID-19 a Najeriya”.

Daga cikin wadannan mutum 204 da aka tabbatar sun kamu a baya-bayan nan dai, 80 a jihar Kano suke, sai 45 a Legas, 12 a Gombe, tara a ko wacce daga cikin Bauchi da Sakkwato, bakwai ko wacce a Borno da Edo, shida a Rivers da Ogun, hudu a Akwai Ibom da Bayelsa da Yankin Babban Birnin Tarayya Abuja, uku a Kaduna, biyu a Oyo da Delta da Nasarawa.

Sai kuma jihohin Ondo, da Kebbi, masu mutum guda ko wacce.

Hukumar ta NCDC ta kara da cewa daga cikin adadin wadanda suka kamu an sallami mutum 319 bayan sun warke, yayin da mutum 58 suka riga mu gidan gaskiya.

A wannan karon jihar Kano ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da Coronavirus a Najeriya.