✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Adadin wadanda suka kamu ya karu da 17

Mutum 17 ne aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya a baya-bayan nan. Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce…

Mutum 17 ne aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya a baya-bayan nan.

Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ce ta fadi haka a wata sanrwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.

“An ba da rahoton sabbin kamuwa da coronavirus kamar haka: takwas a Legas, uku a Katsina, biyu a Yankin Babban Birnin Tarayya, daya a Neja, daya a Kaduna, daya a Anambra, daya kuma a Ondo”, inji NCDC.

Wannan ne ya kai  jimillar wadanda aka tabbatar sun kamu a Najeriya 305 zuwa karfe 9.30 na daren 10 ga watan Afrilu.

“Daga cikinsu an sallami mutum 58, yayin da wasu bakwai kuma suka riga mu gidan gaskiya”, inji NCDC.

Jihar Legas ce dai ke kan gaba da yawan wadanda suka kamu yayin da Yankin Babban Birnin Tarayya ke rufa mata baya,