✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: An samu karin mutum shida

An samu karin mutum shida da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus, lamarin da ya sai adadin wadanda suka kamu a Najeriya ya kai…

An samu karin mutum shida da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus, lamarin da ya sai adadin wadanda suka kamu a Najeriya ya kai 190.

Gaba daya mutum shidan dai a jihar Osun suke, kamar yadda Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta sanar a shafinta na Twitter.

“Zuwa karfe 11.00 na ranar 3 ga watan Afrilu an tabbatar da mutum 190 sun kamu da COVID-19 a Najeriya. An sallami 20 daga cikinsu yayin da biyu suka riga mu gidan gaskiya”, inji sanarwar.

Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan wadanda aka tabbatar sun kamu da kashi 54 cikin 100, yayin da Yankin Babban Birnin Tarayya ke biye mata da kashi 21 cikin 100.