✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: ‘Ba zanga-zanga ba ce ta sa aka sallame mu’

Shugaban masu dauke da cutar coronavirus da aka killace a asibitin garin Kwadom na jihar Gombe, Muhammad Buba, ya ce ba zanga-zangar da suka yi…

Shugaban masu dauke da cutar coronavirus da aka killace a asibitin garin Kwadom na jihar Gombe, Muhammad Buba, ya ce ba zanga-zangar da suka yi ba ce ta sa aka sallame su.

Muhammad Buba, wanda dan asalin garin Damboa na jihar Borno ne kuma har ila yau shugaban masu sana’ar acaba na yankin Koshofe a jihar Legas, ya ce a lokacin da suka yi zanga-zangar wata ce daga cikin su take da rauni a jikinta da yake wari, su kuma suka ga bai kamata a kyale ta ba.

“Saboda girman raunin, yatsu hudu na hannun mutum za su iya shiga ciki, sannan kuma idan ta mutu a wajen za a iya cewa coronavirus ce ta kashe ta”, inji shi.

Ya kuma ce da suka nemi a kula da matar aka ki shi ne suka ta dan yi motsi don su jawo hankalin al’umma da gwamnati a yi mata magani.

‘Dalilin sallamar mu’

“Mutane suna ganin kamar wannan zanga-zangar ce ta sa aka sallame mu – ni kam a sanina ba don wannan zanga-zangar ba ce.

“Muna zaune ne aka zo aka ce mu goma da aka yiwa gwaji sau biyu sakamako ya fito ya nuna wai ba mu da cutar shi ne aka sallame mu”, inji Buba.

Hukumomin lafiya a jihar Gombe ma sun ce ba don majinyatan suna tunanin lafiyarsu kalau aka killace su suka yi zanga-zangar ba.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Ahmed Muhammad Gana, cewa ya yi majinyatan sun yi boren ne saboda sun gaji da zaman kadaici.

‘Ina zaman zamana’

Sai dai har yanzu Muhammad Buba, wanda ya ce shi dan acaba ne a Legas wanda ya dawo Gombe  cikin iyalansa don ci gaba da sana’arshi bayan hana haya da babur a can, bai yarda cewa ya kamu da cutar ba.

“Bayan dawowa ta da mako guda ina zaune a gida kawai sai aka zo aka neme ni aka ce ina da cutar in tafi a killace ni”, inji shi.

Masana harkar lafiya dai sun sha bayanin cewa mutanen da kan kamu da cutar sun kasu kashi uku – akwai wadanda ba sa nuna alamun rashin lafiya, wadanda ake killacewa saboda kada sun yada ta.

Sannan akwai wadanda ke nuna alamu kadan, da kuma wadanda ke yin rashin lafiya mai tsanani da kan hada da zazzabi mai zafi, da sarkewar numfashi, da tari mai tsanani, da ma wasu alamun.

Muhammad Buba ya kara da cewa da aka sallame su an ba su takardar shaidar warkewa daga coronavirus.