✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Coronavirus: Buhari zai yi jawabi ga ‘yan Najeriya yau

Fadar shugaban Najeriya ta ce, shugaba Buhari zai gabatar da jawabi ga ‘yan kasar da yammacin yau  Litinin da misalin karfe 7 na yamma. Mai…

Fadar shugaban Najeriya ta ce, shugaba Buhari zai gabatar da jawabi ga ‘yan kasar da yammacin yau  Litinin da misalin karfe 7 na yamma.

Mai ba shugaba Buhari shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ne ya fitar da sanarwar cewa shugaban zai gabatar da jawabin ne da misalin karfe 7:00 na yamma wanda za a watsa kai tsaye a kafofin watsa labarai na kasar.

Ana kyautata zaton shugaba Buhari zai yi jawabi ne akan annobar coronavirus  da kuma matakan da gwamnati ke dauka, inda ake sa ran watakila ya tsawaita dokar hana fita da shugaban ya kafa a jihohin Lagos da Ogun da kuma birnin tarayya Abuja.