Da Dumi Dumi

Coronavirus: Wadanda suka kamu a Najeriya sun haura 7,500

Wasu ma'aikatan Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC suna aikin raba magunguna da kayan aiki ga jihohi (Hoto: Twitter/NCDC)

Karin 265 sun kara kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya, a cewar hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa NCDC.

Alkaluman da NCDC sun nuna kawo yanzu mutum 7,526 suka harbu da cutar tun farkon bullarta a Najeriya.

Alkaluman da NCDC ta fitar a daren Asabar sun nun jihar Legas ce ke kan gaba da sabbin masu cutar #COVID19 guda  133.

Sauran jihohin da aka samu karin wadanda suka kamu da cutar su ne: 

 • Oyo – 34
 • Edo – 28
 • Ogun – 23
 • Abuja – 22
 • Filato – 6
 • Kaduna – 5
 • Borno – 3
 • Neja – 3
 • Kwara – 2
 • Bauchi – 2
 • Anambra – 2
 • Inugu – 2

Ya zuwa yanzu mutum 2,174 suka warke daga cutar a kasar, baya ga mutum 221 da cutar ta yi ajalinsu.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya