Da Dumi Dumi

Coronavirus: Mutum na farko ya rasu a Adamawa

Ma’aikatan lafiya ne a sahun farko na yakin da ake yi da annobar coronavirus
Mutum na farko ya mutu a jihar Adamawa a sakamakon cutar coronavirus kamar yadda alkaluman Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta NCDC ta fitar suka nuna.
Sanarwar ta ce mutumin da ya rasun yana cikin mutum biyar da suka kamu da cutar a baya bayan nan.
Mutumin ya rasu ne tun kafin jami’an da ke kula da cutar su sami zarafin duba shi, kasancewar asibitin da aka kwantar da shi yana nesa na bmYola, babban birnin jihar.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto mahukunta a jihar ba su kai ga fitar da jawabi kan wannan batu ba.
Sai dai majiyar mu ta shaida cewa an kwantar da marigayin a wani  asibiti mai zaman kansa kafin daga bisani ayi masa gwajin cutar bayan da ya nuna alamun ciwo a kafofin numfashin sa.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya